Connect with us

ADABI

Ingantacciyar Fassara: Fasaha Ko Kimiyya

Published

on

A ci gaba da zakulo wa masu karatunmu makaloli a wannan shafi daga masana daban-daban. A wannan karon ma kamar wasu lokutan shafin ya dauko malakalar Salisu Ahmad Yakasai, mai taken; “Ingantacciyar Fassara: Fasaha Ko Kimiyya”, daga cikin littafin Champion Of Hausa Cikin Hausa, wanda Sashen Nazarain Harsuna Da Al’adun Afirka ya wallafa, domin karrama Farfesa Dalhatu Muhammad.
Gabatarwa
Tarihi ya bayyana irin gwagwarmayar dan’adam wajen amfani da hanyoyin sadarwa daban-daban domin sarrafa da kuma adana ilimin da aka samu daga nahiya-nahiya, ta yadda wasu al’umma za su ci gajiya a nan gaba. A matsayin harshe na hanya ma fi inganci ta sadarwa, das hi ne ake bayyana tunani cikin zubi da tsarin zamantakewa. Babban abin da ka iya zama cikas, a hanyar sadarwa shi ne bambancin da ke akwai tsakanin harsunan duniya. A zamanin nan na yau, sadarwa tsakanin kasashe daban-daban ta mafani da harsuna da yawa na tabbata ne ta aikin fassara.
Domin nazarin ingantacciyar fassara, mun karkasa wannan makala zuwa gida biyar. Da farko dai akwai gabatarwa sashe na farko. Daga nan kuma sai ma’anar fassara a sashe na biyu. A sashe na uku kuwa mun tattara yanayi da tsarin ingantacciyar ne. daga nan kuma sai sahe na hudu a inda muka yi kokarin bayyana matsayin aikin fassara fasaha ce ko kuma kimiyya. Akwai kuma jawabin kammalawa.
Ma’anar Fassara
Kamus din Webster ya bayyana fassara a matsayin musaya sako daga wani harshe zuwa wani harshe daban. Shi kuwa lewis (1958:265) asalin Kalmar ya duba, inda y ace Kalmar “fassara” daga latin aka samo ta, kuma tana nufin “isar da sako”. Foster (1958:1) kuwa ya dauki fassara ne a matsayin wani aiki na isar da sakon matani daga harshen asali (HA) zuwa harshen karba(HK). Ba tare da la’akari da al’ada ba. Catford (1965:20) cewa ya yi, “fassara ita ce musanya matani daga harshe guda da kwatankwacin wannan matani zuwa wani harshe daban. A wannan ma’ana an fi bayar da muhimmanci ga kwatancin matani da za a samar daga wani harshe na daban, sai dai kuma daidaito da ake nema ne bai fito a fili ba.
A ra’ayin leny (1967:148) kuwa “ Fassara yanayi ne na sadarwa wanda manufar ita ce ta sarrafa ilimi daga hasshen asali (HA) domin amfanin bako mai karatu”. Domin bayar da goyon baya ga wannan ra’ayi kuwa. Sabory (1968:37) ya amince cewa fassara na tabbata ne ta amfani da kwatancin hikimar da ke kunshe cikin abubuwan abubuwan da aka bayyana. Wannan ya nuna cewa, aikin fassara al’amari ne da za a iya bayyanawa da yanayin sadarwa ta majiya harsuna biyu domin samar da matani a harshen karba (HK) da zai dace da matani a harshen asali(HA) (Resiss: 1971:1). Haka kuma dangane da ma’anar fassara, ga abin da Brislin (1976:1) ya ce:
A dunkule fassara na nufin musayar hikima da tunani daga wani harshe (HA) zuwa wani(HK), la’alla harsunan a rubuce suke ko a maganance, suna da ka’idojin rubutu ko babu, kuma ko da kuwa daya ko duka harsunan na amfani da kalmomi ne tamkar kurame da bebaye.
A wata mai kamar wannan kuma, Pinhauck (1977:38) ya bayyana fassara a matsayin “Yanayin samar da matanin harshen karba (HK) daga matanin harshen asali (HA)”. Nida (1984:83) shi ma ya bayyana cewa, “Fassara ta kunshi maida kwatankwacin ma’ana da salon sakon harshen asali (HA) domin zama sakon harshen karba(HK)”. Hka ma fassara a ta bakin Beli (1991:398) ta kunshi musayar ma’ana ta matani daga wani harshe zuwa wani.
Ta kowace fuska a kalli batun fassara dai, to ma’ana da matsayi ne ke kara bayyana. Shi Spibak (1992:398) ya dauki fassara ne a matsayin wani “Gagarumin aiki na karance-karance”. Wato matukar mai aikin fassara ba shi da kwazon karatu, to ba zai iya yin adalci ga matanin da aka fassara ba. Hasali ma ai kamar yadda Basset(1994) ya ce, “Ita fassara ta kunshi sabunta matanin asali (HA) cikin tabbatar da dacen ma’anonin biyu, ba tare da haifar da illa ga tsarin harshen matanin asali da kuma na haeshen karba ba”.
A wani ra’ayi na kallon mai fassara a matsayin dan koyo kuwa, Robonson(1997:49) cewa ya yi, “Fassara aiki ne na fikira da kunshi nazari ta hanyoyi daban-daban” wato dai wannan aiki ne na sarrafa basira cikin kowane yanayi na zamantakewa. Su kuwa Hatim da Mason (1997:1) a gudummawarsu ta fahimtar ma’anar fassara cewa suka yi ”Fassara aiki ne na sadarwa tsakanin al’umma mabambanta harshe da kuma hanyar rayuwa” Sai dai kuma a ganin Hourbert (19998:1) a mafi yawan lokuta ana daukar fassara a matsayin “Wani yanayi na bayyana sako daga harshen asali ta yadda masu karatu za su fahimta cikin harshen karba.”
Ta wani bangaren kuma,Nogueira(1998:1) cewa ya yi “ Fassara aiki ne na gina al’umma” idan haka ne kuwa (wanda haka din ne) , to aikin fassara yana da amfani wajen bayyana irin rawar da harshe ke takawa cikin zamantakewar al’umma. Wato dai fassara na iya zama yanayi na shimfida daidaito tsakanin matanin harshen asali zuwa ga na harshen karba. Ba sakka hakan ya kara zama wani yunkuri na fahimtar da mutane tasirin harshensu cikin fa’idantuwa da ilimin da ke kunshe a wani harshe daban. Don haka ne ma Kaur(2005:1) ya ce,”aikin fassara aiki ne na magance matsaloli” Sai dai kuma Sugimoto (2005:1) ya yi amfani ne da falsafa wajen yin bayani game da fassara.
“Fassara wata hikima ce ta musayar lullube ma’ana ko tunani cikin fahimtar zubi da tsarin rayuwa”.
Gaskiyar magana ita ce, a cikn fassara dai na zahirin rayuwa, duk kuwa da matsalolin da ke tattare da ita fassarar cikin amfani da mabambantar harsuna, al’adu da kuma al’umma daban-daban a kawo yanayi na canje-canje da kirkire-kirkire domin samar da bayanai cikin inganta rayuwar al’umma.
Yanayin Tsarin Ingantacciyar Fassara.
Masana daban-daban sun yi ittifaki cewa, akwai dalilai da yawa da kan tabbatar da inganci ko sahihancin fassara. Ga misali, masanin nan Bafaranshe mai suna Dolet a ruwaitowar Miremadi(1993:74) cewa ya yi domin a samar da fassara mai inganci wajibi ne mai aikin fassara ya kauce wa fassarar baki da baki, musamman ma da yake irin wannan fassara tana gurbata ma’ana da kuma armashin sakon da ake son isarwa. Don haka ne ma Tytler (1790) ya jaddada cewa, ingantacciyar fassara, wajibi ne salo da zubi da tsari su dace da mizanin awo na isar da sako.
Shi kuwa Showeman a ta bakin Miremadi (1991:34) ya dauki fassara a matsayin aikata laifi sai dai kuma ga wadanda suka dauki fassara larura da ake bukata a rayuwa, Philmore(1919:4) na ganin fassara tamkar abinci ne da zai gina kuma ya bunkasa harsuna masu tasowa. Ta la’akari da hakan ne ma ya sa Sourter(1920:7) yin ikirarin cewa, ya kamata ingantacciyar fassara ta haifar da sakamako mai kyau a zukatan masu karatu. Kwatankwacin yadda harshen asali (HA) zai yi. Bugu da kari, Belloc (1931:22) ya karfafa cewa ayanayin da tsarin ingantacciyar fassara, dole ne ta kasance yadda za a iya auna sahihancinta yadda abin da aka fassara zai kasance mai inganci.
Dangane da muhmmancin ingantacciyar fassara kuwa,Bates (1943:7) yana ganin cewa,”babu wani al’amari da zai wanzu ba tare da fassara ba” wato babu wata dama ta musayar tunani ko bunkasa fasaha ba tare da taimakon fassara ba”. Sai dai kuma ba kowace irin fassara ce za ta dace da wannan ikirari ba. Saboda haka ne ma Edwards(1957:13) yake cewa,”a koyaushe akwai bukatar yin adalci ga fassara, ta yadda za asamu dandanon matani tamkar a harshen asali (HA). Wannan ra’ayi na Edwards ya samu goyon baya daga Knod (1957:5) wanda ya kara da cewa, “ kamata ya yi aikin da aka fassara ya yi armashi da kuma ya ba da nishadi tamkar dai a harshen asali(SL).
Ko shakka babu, su Edwars(1957) da Knod (1957) sun yi amanna da samuwar sakamako na kwarai cikin isar da sako a matsayin sharadin zama ingantacciyar fassara. Za mu tsaya a nan sai mako na gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!