Connect with us

Madubin Rayuwa

Rashin Yarda Ga Masoya

Published

on

Babban abin da yake kawo rashin yarda ga masoya bai wuce zamani ba, shigowar zamani ne da kuma abubuwan da suke cikin zamanin musamman yadda wasu masoyan ba su da tabbas daga mazan har matan, ban ce duka ba, amma ma fi akasari samun nagari na da matukar wuya a yanzu.
Rashin gaskiya ya rinjayi zukatan masoya, kowanne kokarinsa ya yaudari daya daga ciki, saboda daman soyayyar kowanne akwai dalilin da ya sa ya amince wa abokin soyayyar akwai manufa ta daban wanda yake cikin zuciyarsu wanda ba su bayyana ta ba.
Koda kuwa soyayyar gaskiya ce mutum yake wa abokin soyayyar ta sa sakama kon abubuwan da yake ji a gari da kuma abin da ya samun labari daga wajen kawa ko aboki sai shi ma ya kiyaye kansa ko ta kiyaye kanta ga rashin yarda da wanda take so ko yake so don kar a kai mutum a baro.
Sai ka gama yarda da namiji ka danka masa so da kauna da amana ko shi namijin ya yarda da macen ya danka mata amana karshe kuma a kai mutum a baro, Hausawa na cewa “Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, toh sai ka shafa wa naka ruwa” wannan dalilin na daya daga cikin dalilan da suke kawo rashin yarda ga masoya.
Rashin yarda tana karanci a yanzu sabda samun na gari wanda yake da tabbacin aure da wuya, in dai ba mutum ya ga bikin za a yi ba toh! Da wuya a yarda da juna wasu ma sai sun ga tabbacin eh! Ga su sun tare gidan mutum ko ya ga ya aureta tukunna hankalin kowanne zai kwanta sai su fara yarda da juna.
Muddin ba aure a kai ba zuciyar masoya tana cikin taraddadi da rudani saboda kowanne gani yake kamar ba soyayyar ce da gaske ba wannan shi yake dada kawo rashin yarda tsakanin zukatan masoya.
Wasu mazan ne ba tabbas! Kamar yadda su ma wasu matan ba su da tabbas! ba tukwane ba bare mutum ya ce zai kwankwasa, wadanda ba nagari ba sun rinjayi na garin kowa gani yake kamar kowanne ma haka zuciyarsa take an yi kudin goro an hada da na garin da wanda ba na garin ba duk an yi jama’u da su, shi ya sa sai a rasa gane masu gaskiya da marasa gaskiya cikin soyayya wannan ya sa babu yarda tsakanin masoya kadan ne ake samun masoyan da suka yarda da junansu a yanzu.
Saboda wasu sai an gama kai kudi da komai sai kuma a ji zance ya sha bamban kida ya canja rawa ma ta canja, wasu ma har sai an saka ranar aure karshe ya ce a dawo masa da komai nasa wanda ya kai idan aka yi bincike sai a ga wata ya samu ta daban wadda yake ganin tafi masa, amma fa wadda ya bari babu wani makusa tare da ita kawai canjawar zuciyarsa ce.
Ta daya bangaren ma ana samu su ma matan sai an kusan biki sai su ce an fasa idan daman iyayen yarinyar ba dattijawa ba ne wato na arziki ba ne musamman in aka samu kwadayayyu lashe moni masu son abin duniya da zarar wani ya fito wanda ya fi wanda za su ba wa aure sai zance ya canja su ce sun fasa.
Ire-iren wa ‘yan nan abubuwa da suke faruwa a wannan zamanin ya sa a yanzu rashin yarda ya fi yawa ga masoya ba a fiya yarda da juna ba, don kowanne gani yake baki ne ya furta ba zuciya ba.
Kwarai kuwa saboda wasu suna da wasu ‘yan matan a gefe guda wanda suke so amma da an samu wata sai a kuma kalailaye ta da kalaman so da kauna da zummar ita kwal tilo zuciyar take muradi har ana dada watsa mata wasu kalamai masu jawo hankalinta don ta amince cewar ta fi kowacce mace a duniya baki daya rashin samunta zai iya jefa shi halin ha’ula’i, wani sa’in ma har ya dada kwarara mata kalaman kauna cewar rashin ganinta ya sa ya kasa cin abinci tare da dagewar jiya fa ko bacci bai yi ba saboda yawan tunaninta.
Sai ya gama kalaman sace zuciyarta tsaf! Tun ba ta amince ba har ta amince karshe kuma ta ji sabon labari wanda kunnuwanta ba za su iya jiye mata su ba, cewar ba ita kadai yake so ba ‘yan matan da yake zarya a gidansu ba su da adadi wani sa’in ma in ta samu tagari da idanuwanta za ta nuna mata komai ta wani fannin ma ta jawo ta gidansu ranar da zai zo don kawai ta ganewa idonta ta kalle shi tsaf! ba tare da ya san ta gan shi ba, ya gama zancensa ya tafi ta dawo tana da ta sani ba ta mallaka masa zuciyarta ba.
Idan aka yi duba kuma ta bangaren su ma matan kusan hakan ne wasu babban burinsu a ce suna da samari bir jik! ba kama kafar yaro, wancen tana da saurayi adadi kaza, shi ne kawai burinta amma fa ta yadda za ta hada samarin ita da kanta take binsu tana cewa tana sansu, daya bayan daya tana zaga wa tana nuna masa babu ya shi amma kuma a gefe guda tana hada samarinta ba adadi ne don kawai burinta ya cika.
Babban abin da zai ba ka takaici shi ne, shi fa saurayin da take so bai son da wadancan wanda take bi tana cewa tana son su suba haka zai ji wani girma ya karu a kansa mace da kanta ta budi baki tana sonsa karshen haduwarsa ya zo cikin rashin fahimtar kudurinta zai ci gaba da bin ta yana zaga ko’ina cewar ita ce wadda yake so, haka sauren ma kowanne zai ta bi yana cewa wance yake so.

SAKONNIN MASU KARATU
Makon da ya gaba ta na yi tambaya a kan cewa: “Wadanne Hanyoyi Masoya Ma’aurata Za Su Bi Don Samun Farin Cikinsu Cikin Auren?” Na kuma samu amsoshi kamar haka:

Rabi’u Bamanga Naira:
Assalamu Alaikum, Hanyoyi da ya kamata ma,aurata su bi domin samun farin ciki nada yawa ga su kamar haka:
-Rikon amana da juna wato rike sirri tsakaninsu na iya sa zamansu ya dore cikin farin ciki da annashuwa
– Tausayawa juna shi ma wani babban lamari wanda yake da muhimmanci a zamantakewar ma’aurata sannan kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen kawo farin ciki tsakanin ma’aurata
-Girmama iyaye wannan shi ma wani abu ne mai muhimmanci matuka a zamantakewar ma’aurata sannan yana da matukar amfani wajen kawo farin ciki.
-Girmama dangi ma’ana mace ta mutunta dangin mijinta haka shi ma miji ya mutunta dangin matarsa wannan shi ma yana da muhimmanci sosai a zamantakewar aure sannan kuma yana kawo farin ciki sosai.
– Biyayyar miji da mata in dai suna yi wa junansu biyayya to zai kara musu kauna da kuma farin ciki a zamansu na aure sosai.
Kadan daga abubuwa da ke kawo farin ciki a tsakanin ma’aurata ke nan.
Rabi’u Bamanga Naira Gombe State 08163277028

Nazifi S.Nuhu:
Aslam Hanyoyin dai ba su da yawa sai wahalar bi, hanya ta farko ita ce kusantar junansu da kuma nuna kulawa ta mu-saman yawan yin wasa da dariya a tsakani sanan da kuma aikata wasu muhiman abubuwa tare kamar su cin abinci ai-kace-aikacen gida da sauransu, ‘yan’uwa sanan sai kuma kautar da kai daga komai na jin bacin rai ta hanyar inganta kowane irin farin ciki yau matarka ta bata maka rai yi kokari ka sa hankali a kan abin mai da shi wasa ita ma za ta dauka a haka ko da kuwa ranka ya baci sosai, aikai baba ne, idan kai ka bata mata kokarin ka ba ta hakuri ta hanyar wasan nan dai ita ce taka lalai hakan akwai riba
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!