Connect with us

RAHOTANNI

Zance Barkatai Na Zubar Da Kimar Matan Aure

Published

on

Duk da irin darajar da Allah ya yi wa mata da kuma yadda addini ke tattalinsu tare da yi masu rangwame kan wasu abubuwa domin raunin da suke da shi, amma zamani ya zo da wata irin wayewa da Bahushe ke kallo a matsayin ci gaban mai hakan rijiya.
A kodayaushe idan ana maganar kunya da mutuntaka an yi ittifaki cewa, mata musamman matan Bahaushe na sahun gaba idan dai batun kunya ake, amma yanzu wannan ya zama labari domin yanzu wasu matan sun sauka daga kan irin waccan kyakkyawar tarbiyya da aka gada iyaye da kakanni.
Babban abin haushi da bacin rai ma shi ne yadda matan aure suka mayar da kasuwannin kamar gidajensu, ta yadda za ka ga cilkakkiyyar matar aure ta saki baki tana ta rakadi tare da mutanen da bai kamata a ce matar aure ce ke irin wannan gaganci ba. A lokuta da dama za ka tarar firar ta wuce maganar ciniki har ta kai mace na ba da labarin mijinta ko wata mu’amala da ya kamata a ce matar aure ba a ji irin wadannan kalaman sakin bakinta ba, da kuma rashin kunyar da ba a saba ganin ainihin matar Bahausahe da ita ba, musamman yadda za ka ga mace ta fitar da nono tana shayar da yaro a tsakiyar kasuwa, a cikin motar haya ko a-daidaita-sahu.
Domin jin taba kin masana akan irin wannan harka, Jaridar LEADERSHIP A YAU ASABAR ta samu zantawa da mataimakiyar Kwamnadan Hisba ta Jihar Kano Hajiya Zahra’u Umar wadda ta bayyana cewa wannan ba al’adar Musulmi ba ce, kuma ma ai rashin mutunta kai ne a ce matar aure ta fito da wani bangare na jikinta a gaban wanda ba muharraminta ba. Sannan kuma yin surutu barkatai ba a son matan Hausawa musamman Musulmi da su ba. Domin abin da aka fi kwatanta matar Bahaushe da shi, ita ce kunya. Wadda mu a sanin mu idan matar aure ta nufo wurin da maza suka taru har hardewa take saboda kunya, amma yanzu sai ka ga mace ta saki baki acikin motar haya ko a tsakiyar kasuwa tana zuba zance. Wannan ko kadan bai dace ba.
Malama Zahra’u Umar tace wannan ce tasa a lokuta da dama muke gabatar da tarukan karawa juna sani, musamman ga mata kan irin wannan matsala domin fadakar da matan muhimmancin kama kai. Ko a cikin gida akwai bukatar mace ta san irin maganar da zata daga murya akanta, tunda addini ya nuna muryar macen arziki ma tamkar al’aura ta ke. Saboda haka muke jan hankalin mata da cewar Kasuwa ba wurin sakin jikin matar arziki ba ne, haka kuma akwai abinda ke tayar mana d ahankali daukar kananan yara a goye a fada kasuwanni da su.
Shiga Kasuwar da mata ke yi da kananan yara bakarmar azabtar da yara ake ba, da farko dai ga cunkoson mutane, ga kuma zafi sannan ga yadda turmutsutsu ke wahalar da yara, don haka idan ya zama dole sai kin shiga kasuwar akwai bukatar ke aje yaron ki a gida domin kaucewa irin waccan matsalar.
Alhaji Sunusi Umar Ata guda ne daga cikin ‘yan Kasuwar Kantin Kwari da ke Jihar Kano, kasuwar da ke karbar bakuncin mafi yawancin matan dake da al’adar shiga kasuwa domin sayayya, kasancewar wannan Kasuwa ce ta kayan da mata suka amfani da su musamman leshi, atamfu, material, mayafai da sauransa, Ata ya bayyanawa Jaridar Leadership A YAU ASABAR cewa duk wani mai kishin kansa da iyalansa hankalinsa in yakai dubu a tashe yake idan ya ga yadda ake gogayya da mata a cikin kasuwanni.
Ata ya ci gaba da cewa, musamman ire-iren wuraren mu da ke kunshe da kalar kayan da mata suka so, za ka yadda mace za ta shigo kantinka, da ta shigo abin zama za ta nema ta sauko da goyon da ke bayanta ta ciro nono ta sa a bakin danta ta ci gaba firar sayayyar abin da ya kawo ta, musamman idan aka yi dace kantin naka akwai fanka mai ratsa barage, sai ka sun baje kolin firarsu idan ma ba a yi sa’a ba wata har gyangyadi zaga ta fara.
Wannan kokadan ba daidai ba ne, idan ya zama dole kin shigo kasuwa to akwai lokacin da ya kamata matar aure ta farmaki kasuwar kafin cikarta, musamman wajen safiya kafin rana ta take, sai ki yi sayayyarki ki fice wani ma bai san kin shiga Kasuwa, amma mace ta shiga Kasuwa tsakiyar rana ko yamma tayi a wasu lokutan ma anfara kokarin hade kaya, sai ka ga wasu sun shigo rumfarka, sannan kuma gashi su basu iya abubuwa cikin hanzari ba. Ata ya ce lallai akwai bukatar mata su san darajar da Allah ya yi masu su kuma dage wajen kare mutuncinsu.
Wata mata mai sana’ar sayar kanyan anko, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaidawa Jaridar Leadership ayau Asabar cewa yin sana’a ya zama wajibi ga mata, kuma a wasu lokuta dole ke sa su shiga kasuwar domin ba wanda zai dauki nauyin yi maka wannanaiki, ganin yadda zamani ya sauya yanzu rayuwa ta zama hannu baka hannu kwarya, wasu matan zawarawa ne miji ya gagara samuwa, wasu kuma mutuwa akayi akabar masu marayu da sauransu, wannan tasa dole mace tashi haikan domin neman abinda zata rufawa kanta asiri.
Matsalar mata acikin ababan haya wannan wata matsala ce mai zaman kanta, domin alokuta da dama zaka tarar masu tukin ababan hawan na amfani da irin damar da suka samu shiga cikin firar da wasu matan keyi, sannan kuma ita kanta firar mace hadari ne da ita domin cikin kankanen lokacin mace kan iya daukar hankali duk wani namiji, saboda haka abinda ake fa a dais hi ne kyautata niyya tare da tsarkake zuciya, mace ta sani akwai abubuwa da dama wanda addinin musulunci ba amincewa mace yin sa ba, kamar yadda sauran al’adu ma suka yi hannun riga da ire iren wadancan abubuwa da ka iya zubar da kimar mace ako da yaushe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!