FIFA Za Ta Dakatar Da Najeriya Daga Kwallon Kafa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

FIFA Za Ta Dakatar Da Najeriya Daga Kwallon Kafa

Published

on


Shugaban hukumar kwallon kwafa ta duniya FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana cewa idan har hukumomi aNajeriya basu daina shiga harkokin wasanni ba a kasar hukumar ta FIFA zata dakatar da Najeriya daga harkokin kwallon kafa.
Shugaban yayi wannan gargadi ne bayan da akayi masa tambaya akan rikicin dayakici yaki cinyewa a neman shugabancin hukumar kwallon kafar kasar nan bayan da wata kotu a kasar nan ta tabbatar da Chris Giwa a matsayin shugaban hukumar.
Tun bayan da kotun tabawa chris Giwa wannan dama yanzu shine shugaban hukumar kwallon kafar kasar nan a babban ofishin hukumar dake babban birnin tarayya Abuja kuma shine yake gudanar da duk wasu ayyuka na shugabanci.
“Kamar yadda muka sani a baya Amoju Pinnick ne shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya saboda shine wanda wakilan kwallon kafar kasar suka zaba kuma mu a hukumance dashi muke aiki” in ji Infantino
Shugaban yace idan har hukumomi basu daina saka siyasa a harkar kwallon kafa ba tabbas kasar zata fuskanci hukunci mai tsanani na dakatarwa kuma na lokaci mai tsawo.
“Mu na da dokoki da tsare-tsare a hukumar kwallon kafa kuma bazamu yarda wani abu da bana kwallon kafa ba ya shigo ya bata mana tafiya saboda haka zamu dauki matakin dakatarwa akan Najeriya.
Ya cigaba da cewa “Amoju Pinnick yana kasar Rasha yana aiki tare damu a ,matsayin wakili kuma shine wanda muka sani a mastayin shugaba bamu san wani ba saboda hakane ma yasa mu ka ba shi aiki a Rasha’
Najeriya dai ta dade tana fama da rikicin shugabancin hukumar kwallon kasar kuma sau da dama hukumar ta FIFA tana gargadin kasar akan irin wannan rikici.

Advertisement
Click to comment

labarai