Juyin Mulki Ga Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASIKU

Juyin Mulki Ga Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Published

on


Na yi mafarki cewa nan da wani lokaci me zuwa, yara samari da ‘yan mata za su fita kan tituna saboda murnar ranar 5th ga watan Yuli ta 2018 a matsayin ranar da aka ware domin hutu a kan yaki da cin hanci da rashawa. A wannan rana ne shugaba Muhammadu Buhari, wajen saka hannu a sabuwar doka ta shugaban kasa ta 6 ya ke cewa “Akwai kyakkyawar alaka tsakanin cin hanci da rashawa, da zaman lafiya da tsaro. Amma abin takaici shine cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a ma’aikatun gwamnati da duk wani sashe na al’umma. Babu tantama cewa, cin hanci da rashawa na yin barazana ga zamantakewa, tsaron kasa da tattalin arzikin Nigeria” Shugaba Buhari ya kara da cewa “Na sa hannu a kan doka ta 6 ta 2018 wadda za ta tsayar da hadahadar kudade ko kadarori da ake zargi ko ke karkashin bincike a kan cin hanci da rashawa yadda marasa gaskiya ba za su iya amfani da haramtacciyar dukiyarsu ba wajen ci gaba da munanan ayyuka na hanawa ko razanar da sashen shari’a a game da ayyukan ta’addanci, samar da kudin ta’addanci, garkuwa da mutane, tunzura rikicin addini ko kabilanci, yi wa tattalin arziki zagon kasa da laifukan da suka jibanci hada-hadar kudade wadanda su ka hada da kassara tattalin arzzikin Nigeria a maimakon kare shari’a da samun jin dadin ‘yan Nigeria”
Cin hanci da rashawa a Nigeria ba zai iya misaltuwa ba kuma wannan doka an dade da bukatar ganin an samar da ita kuma ta fara aiki, domin a baya sashen majalisa ya sanyawa dokar samar da hukuma me zaman kanta don kwatowa Nigeria dukiyoyi na haram daga hannun mutane, amma kuma shiru kake ji.
A kiyasi na baya bayan nan, akwai kimanin Dalar Amurka Biliyan $100 dake tattare da wasu daidaikun mutane da ake tuhumarsu a kasar nan. Ganin yadda shari’u ke tafiyar hawainiya, za’a iya daukar shekaru da dama kafin a warware wadannan shari’u. Musamman idan mu ka yi la’akari da yadda shari’un Jolly Nyame da na Joshua Dariye suka dauki tsawon shekaru goma sha daya ana tafka su.
A cikin irin wadannan manyan badakaloli na cin hanci da rashawa mun ga yadda ake tuhumar karkatar da kimanin Dala biliyan $20.2 daga kamfanin mai na kasa NNPC. An fitar da wannan badakala cikin rahoton hukumar National Edtractibe Industries Transparency Initiatibe tsakankanin shekarun 1999 zuwa 2012.
A shekarar 2006 babban bankin kasa CBN ya fitar da Dala $7 daga cikin asusun kasashen waje na Nigeri sannan ya sa ka kudaden a cikin asusun bankuna 14 da suka kusa durkushewa. Haka nan ya sa ke bada tallafin Naira biliyan =N=600 (kimanin dala biliyan $4) ga wadannan Bankuna 14 amma har kawo yau CBN ba ta karbo jumillar dala biliyan $11 ba. Suna ina? Ranar 6 ga watan Satumba na 2016 a ka gama shiri tsaf, domin kamfanin NNPC ya karbo wasu kudade kimanin dala biliyan $9.6 a matsayin haraji da aka samu na cinikayyar danyen mai na tsarin cinikin bani-gishiri-in-baka-manda, duk da cewa wasu majiyoyin sun ce an karbo kudin, amma asusun gwamnatin tarayya bai ga ko taro ba.
Akwai bashin dala biliyan $1.9 cikin dala biliyan $2.5 da a ke bin kamfanin mai na Mobil wanda ya dace ya biya gwamnatin tarayya a matsayin kudin rijiyoyin mai gudi uku da aka bashi lasisin su, amma har yanzu ba su biya ba. Haka ma kamfanin kasar Chine wato ZTE, a shekarar 2009 ya karbi kudi kimanin dala miliyan $470 don samar da na’urar daukan hoton (CCTB) a garuruwan Abuja da Lagos, amma bai aiwatar da kwangilar ba kuma ba’a dawo da kudin ba. Akwai kuma wasu kudaden kimanin dala biliyan $12.7, wato ribar gangar mai miliyan 60.2 wadanda ake zargin kamfuna sun sace su ka fita da shi zuwa Amurka aka sauke wannan adadin mai a tashar jirgin ruwa ta Philadelphia tsakankanin watan Janairu na 2011 zuwa watan Disamba na 2014 kuma ba’a bada ba’asinsu ba. Haka nan akwai kudade kimanin dala biliyan $13.9 wadanda kamfanin MTN ya fitar ba bisa ka’ida ba daga bankunan Nigeria duk da cewa dai gwamnati ta ci tarar kamfanin dala bilyan 5 wadda daga baya su ka biya dala biliyan $3.
Sauran caje-caje na badakalar kudade sun hadar da na Diezeni kimanin dala bilian $20, da na Sambo Dazuki dala biliyan $2.1 wadanda wani rahoto ya nuna cewa sun kai dala biliyan $15. Akwai Naira biliyan 4.7 da ake cajin Musliu Obanikoro, da Femi Fani kayode Naira biliyan 4.7, Dikko Nde Naira biliyan 40, Nenadi Usman Naira biliyan 1.5, Raymond Dokpesi Naira biliyan 2.1, Aled Badeh Naira miliyan 800. Akwai kuma irinsu Ike Ekweremadu, Peter Nwoboshi, Buruji Kashamu, Ahmed Sani Yerima, Dabid Mark, Stella Oduah, Danjuma Goje, Abdulaziz Nyako, Jonah Jang, Sule Lamido, Ibrahim Shema, Ibrahim Shekarau, Orji Kalu, duk kana cajin su da badakaloli daban daban.
Idan ka tattara wadannan badakaloli, a jumlace sun haura Dala biliyan $100 kuma kwato su hannun wadanna mutane zai dauki shekaru sannan suna iya mutuwa domin mun ga yadda Aliyu Akwe Doma da ake caji ya mutu don haka an yi asarar abinda ake nema wajensa. Wannan dalili ya sa shugaba Buhari ya saka hannu a waccan doka ta shida domin bawa gwamnatin tarayya karfin ikon kwace dukiyar da ake zargi ta haram ce, ko a daskarar da ita a banki yadda mutum ba zai iya tabawa ba. A maimakon al’umma su yi asara sakamakon mutuwa ko tsaikon shari’a, yanzu duk wanda ake zargi sai a kwace ko daskarar da dukiyarsa shi kuma ya tafi kotu domin nuna shaidar cewa dukiyarsa ce ta halal kuma ga yadda ya yi ya same ta. Idan ba Nigeria ba ina zaka ga mutanen da ba su taba zuwa kasuwa ba ko yin kowanne irin ciniki amma ka gansu da biliyoyin daloli, ina suka same su? Don haka su je kotu su yi bayani.
Irin wannan yunkuri da Buhari ke yi na neman ceto al’ummar Nigeria, shi ya sa azzalumai su ka yi gungu wajen ganin sai sun hana shi dawowa a karo na biyu domin sun tabbatar ba za su tsira da dukiyoyinsu na haram ba. Su na amfani da kudadensu wajen tunzura tarzomar makiyaya da hada fitina tsakanin kirista da musulmi na arewa duk a kokarin ganin ta haka za su sa Buhari ya fadi zaben 2019.
Ta irin wannan doka, idan ba mu manta ba a baya itace shigen hanyar da wannan gwamnati ta bi wajen samun nasara a kan yaki da Boko Haram. Domin ta datse hanyoyin da ake samarwa kungiyar kudade shi ya karya ta, don hakan wannan doka mu na ganin ita za ta karya azzuluman da su ka sace mana kudade su ka mai da ‘yan kasa fatararru. Idan aka datse musu kudade ma ga yadda za su rika daukar dawainiyar tunzurin rikice rikice.
Yaki da cin hanci da rashawa abu ne da ya fi karfin gwamnati ita kadai dole kowa ya saka hannunsa a ciki idan ana son cimma nasara. Amma idan ka duba sai ka ga hannaye nawa ke bada gudunmuwa? Ma iya cewa akwai hannu daya da rabi. E mana, hannu daya da rabi, domin daga hannun shi Shugaba Buhari sai rabi, wato na ‘yan kalilan masu kishin kasar da ba su taka kara sun karya ba. Cin hanci da rashawa na da fuskoki daban daban, bari na baku misali. Ina da aboki wanda a yanzu haka ya zama mai bawa shugaba Buhari shawara. Tun shekarar 2003 ya ke harkar Buhari kuma mai karsashi ne a cikinta. A baya zai wahala ba ka ji muryarsa a gidajen rediyo ya na yada Buhariyya ba, sannan wakokin sa sun cika ko’ina ya na wa Buhari kamfe. Amma abin takaici tun da aka ba shi mukami ya koma Abuja, hana rantsuwa sau daya, kuma shima sau dayan sai da na chase masa sannan ya zo ya yi hira ta awa guda da gidan wani talabijin. Na sa an bashi lokaci ya ki zuwa a karo na farko sai da na kira shi na tuna masa cewa kada ya manta a baya shi ake ji ko’ina kafin a sami gwamnati amma yanzu an samu ya yi kus. Kar ka manta wannan taliki idan ka ziyarci shafukansa na sada zumunta kullum cike su ke da hotunan shi da na manyan mutane a kasashen duniya, abinda ya dame shi kenan ba yada manufar gwamnatin da yak e aiki ba. Kasancewar an bashi wannan dama kuma mutanensa na bukatar bayanai da za su wayar musu da kai game da abubuwan da mai gidansa ke kokarin gina wa al’umma amma ya kasa, shin wannan ba daidai ya ke da rashawa ba?
A karshe ya kamata talakan Nigeria ya gane cewa, manyan nan namu za su iya sadukar da rayuwarsu da ta kowa domin kare abubuwan da suka mallaka sakamakon mayar da talaka bawa, amma shi talaka me ya ke da shi da shi da zai yi asara? Amma talaka ya sani cewa shi ne zai fi kowa morewa idan aka kawar da cin hanci da rashawa. Amma abin takaici bai san haka ba domin a kwanan nan mun ga yadda ranar da aka gurfanar da Ibrahim Shekarau da Aminu Wali a kotu, yadda talakan da bai san kansa ba ya yi kokarin zanga-zanga don kare wadannan mutane biyu, tare da manta cewa wadannan mutane a na tuhumarsu ne da raba kudin makamai a lokacin da ake kokarin yakar annobar Boko Haram. Sakamakon wannan kashe mu raba da su ka yi, mutane da dama sun rasa ransu, yara sun zama marayu, mata sun zama zawarawa, sojojinmu sun rasa sassa na jiki ko rayukansu ban da wasu tulin matsaloli da hakan ya haifarwa al’umma da tsawon lokaci zai addabi al’ummar. Mu sani cewa da ni da kai da su da kowa muna da gudunmuwa daidai gwargwadon da zamu iya bayarwa wajen yakar cin hanci da rashawa. Baba Buhari dai ya fada ma na cewa “Dole mu tashi mu murkushe cin hanci da rashawa a kasarmu, ko kuma cin hancin da rashawa ya murkushe mu?”

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!