Zaben Ekiti: APC Da PDP Sun Shata Dagar 2019 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Zaben Ekiti: APC Da PDP Sun Shata Dagar 2019

Published

on


• ’Yan takara sun lashe mazabunsu
• An yi nasara da kashi 90% – INEC
Daga dukkan alamu zaben jihar Ekiti da a ka gudanar a jiya Asabar, 14 ga Yuli, 2018, ya dasa danbar babban zaben kasa da za a gudanar a shekara mai kamawa, wato 2019, a yankin Kudu maso yammacin Najeriya a tsakanin manyan jam’iyyu biyun da ke hamayya da juna, APC da PDP.
Tun da fari dai, ’yan takarar manyan jam’iyyun guda biyu sun lashe mazabunsu da irin rinjayen da su ke bukata.
Dan takarar jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar ta Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya lashe akwatinsa mai lamba 9 na mazabar Isan da yawan kuri’a 186, inda ya tika dan takarar PDP, Farfesa Kolapo Olusola Eleka, wanda ya samu kuri’u biyu kacal, yayin da ba a yi amfani da kuri’u 145 daga cikin kuri’un da a ka yi rijista 345, inda daga ciki jam’iyyar APA ta samu kuri’a daya kacal.
Shi ma dan takarar na PDP, Farfesa Eleka ya dauki fansa a kan Dr. Fayemi, inda ya lashe nasa akwatin mazabarsa da kuri’a 452, yayin da dan takarar APC din ya samu kuri’u 105, yayin da jam’iyyar DCP ta samu kuri’a daya kacal, APA ita ma daya, PANDEL ma daya, sai kuma PPA mai guda uku.
Tsohon gwamnan jihar kuma dan jam’iyyar Apc, Mista Segun Oni, shi ma ya lashe zaben a nasa akwatin da kuri’a 129, inda ya bai wa PDP tazara, wacce ta samu 103.
Sanata mai ci na jam’iyyar PDP, Sanata Biodun Olujimi, ya samu nasarar kawo akwatinsa da kuri’u 147, yayin da APC ta samu kuri’a 111.
Tuni dai Apc ta kayar da dan takarar jam’iyyar SDP, Mista Akin Ayegbusi, a kwatinsa da kuri’a 104, yayin da PDP ta samu kuri’a 72, ita kuwa SDP din ta samu tara kacal.
Shi ma dan takarar mataimakin gwamnan jihar a karkashin tutar jam’iyyar APC, Mista Bisi Egbeyemi, ya samu nasarar kawo akwatinsa da kuri’a 177, yayin da ya bai wa PDP kashi da wacce ta samu kuri’a 130.
Duk da cewa an samu sa-toka-sa-katsi a wasu guraren, amma a nata bangaren, hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta bayyana cewa, an samu gagarumar nasarar a yayin gudanar da zaben da kashi 90%.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Abdulganih Olayinka, a yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a Ado-Ekiti lokacin da ya ke batu kan gudanar da aikin, ya na mai cewa rahotanni daga dukkan kwamishinoni takwas da ke bakin aiki a sassan jihar.
Olayinka ya ce, ya yi matukar farin ciki da jin cewa dukkan ma’aikatan INEC, ciki har da na wucingadi, sun isa guraren aikinsu a kan kari kuma sun aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.
“A karamar hukumar Agboyin ne kawai an samu rahoton kwacen kuri’a, sai kuma gurare biyu ko uku da na’ura ta samu matsala,” in ji shi, ya na mai karin haske da cewa tuni a ka maganta wadancan matsalolin.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!