Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Annobar Ambaliya Ta Kashe Mutum 11 A Ogun

Published

on

Kimanin mutane sha daya ne suka rasa rayukan su kuma dukiyoyi na miliyoyin kudi da dama suka salwanta a ranar juma’ar da ta gabata a garin Abeokuta cikin jahar  Ogun, sakamakon iftila’in annobar ambaliya.

An fara ruwan sama ne a garin da misalin karfe 4.30 na yammacin ranar wanda kuma ya kai har tsawon awowi uku kafin ya dauke, inda hakan ya janyo jerin gwanon ababen abin hawa a cikin garin har wasu suka suka daba a sayyardar su don zuwa gidajen su.

Daga cikin wadanda suka rasa ‘yan uwan su harda wata mai sayar da abinci Halirat Akintobi, da kuma ‘yanyanta biyu maza, inda acewar wata majiya mariganyiyar tana sayar da kwantaina ce da take sayar da abinci a yankin Ilawo, kusa da Kobiti a gefen babban masalacin juma’a dake  karamar hukumar  Abeokuta ta Arewa.

Ance tana cikin kwantainar ce tare da ‘yayan nata biyu lokacin da lamarin ya auku an kuma tsamo gawar su ne a cikin wani rafi tuni kuma aka bizne su kamar yadda shari’ar Musulunchi ta tanadar.

Wata majiya ta bayyana cewar, har yanzu wasu mazaunan yanki suna ta kai gauro da mari wajen neman ‘yan uwan su da ambaliayr ta rutsa da su, inda kuma ake ci gaba da zuwa gidajen yan uwan da lamarin ya shafi yan uwan su don yi masu ta’aziyya.

Baya ga mai sayar da abincin da ‘ya’yan ta da aka bizne, har ila yau, wasu gawarwaki takwas da ambaliayr ta rutsa da su an kai gawarwakin dakin ajiye gawa na babban asibitin dake Ijaiye cikin garin Abeokuta.

Shugaban kungiyar  Red Cross Society reshen jahar ta Ogun Mista Joseph Obalanlege,ya bayyana cewar lamarain ya munanan matuka, inda ya tabbatar da cewar mutane takwas ne suka mutu. Ya kara da cewa, mun kai gawarwaki takwas zuwa asibiti.

Ya kara da cewa, kimanin ababen hawa takwas ne ambaliyar ta yi awon gaba da su  bayan da Kogin Ogun dana  Sokori suka yi ambaliya zuwa cikin garin.

Yankunan da lamarin yafi aukuwa sun hada da, Ijaiye, Kuto,  Lafenwa, Oke Lantoro, Amolaso, Kobiti da Ilawo da sauran su.

Da take fadar nata bangaren akan lamarin wata ‘yar kasuwa a yankin  Amolaso Bisola Somuyiwa, wadda take ta yin kuka har zuwa lokacin kammala hirar da manema labarai suka yi daita ta ce, ta yi asarar komai harda sahgunta.

Acewar ta, “ na  kai tsawon shekaru goma ina sayar da barasa da kuma sauran kayan kawalba a yankin shaguna na guda biyu ne kuma a loakcin da aka fara ruwan baiyi wani karfi  saosai ba a hankali sai ya dinga karuwa ya yi karfi sosai.”

Sauran wasu mazauna yankunan wanda idanuwan su suke cike da hawaye a lokacin da suke kwashe kayan da suka tsira da su daga shagunan su da kuma gidajen su.

Wani bene mai hawa biyu shi ma lamarin ya shafe shi harda wani sabon otel sabo da aka kammala shi dake kusa da gabar rafin  Sokori  ambaliyar ta rusa shi .

A ziyarar gani da ido da kwamishinan ‘yan sandan jahar Ahmed Iliyasu ya kai a yankin Amolaso, ya shedawa manema labarai cewar har yanzu yana yin nazari akan iftila’in don tantance mutanen da lamarin ya rutsa da su.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: