Fadar Shugaban Kasa Ta Musanta Cewa Sheriff Ne Babban Daraktan Kwamitin Buhari 2019 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

MANYAN LABARAI

Fadar Shugaban Kasa Ta Musanta Cewa Sheriff Ne Babban Daraktan Kwamitin Buhari 2019

Published

on


Bayan awanni 20, fadar Shugaban kasa ta musanta kalaman babban mai taimaka wa Shugaban kasa kan harkokin siyasa, Gideon Sammani, kan sanarwar da ya bayar na kasantuwar tsohon shugaban Jam’iyyar PDP, Sanata Ali Modu Sheriff, a matsayin babban daraktan kwamitin kamfen na Buhari 2019.

Fadar ta bayyana sanarwar a matsayin wacce ba a bayar da izinin yin ta ba, wacce ta ce kowa ya yi watsi da ita.

Daraktan hulda da manema labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Lawrence Ojabo, wanda tun a can baya ya tabbatar wa da manema labarai yin nadin, a ranar Asabar kuma sai ya ce, “Hankalin ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya kai kan wata sanarwa da ake ta yawo da ita a kafafen yada labarai, wacce babban mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin siyasa ya bayar, inda a cikinta ya bayyana wasu sunaye biyu a wasu mukamai a kwamitin da ke goyon bayan sake takarar shugaba Buhari a 2019.

“Ya zama tilas a bayyana wa ‘yan Nijeriya da kuma musamman ‘yan APC cewa wannan sanarwar ba wanda ya bayar da izinin yin ta, don haka kowa ya yi watsi da ita.

“Ana kuma bin dukkanin matakan da suka kamata wajen ganin ba a sake maimaita irin wannan sanarwar ba a nan gaba.”

A sanarwar ta ranar Juma’a, Sammani ya bayyana Ali Modu Sheriff, wanda ya yi gwamna a Jihar Borno har karo biyu, ya kuma canza sheka zuwa Jam’iyyar ta APC makonni kadan baya, a matsayin shugaban kwamitin.

Ya kuma bayyana cewa, wannan kwamitin daban yake da kwamitin yakin neman zabe na, ‘Buhari Campaign Organisation (BCO), wanda a yanzun haka yake karkashin shugabancin Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi. Sa’ilin da Lauyan nan mai kare hakkin dan adam, Festus Keyamo, yake a matsayin kakakin kwamitin, kuma daraktan sa na tsare-tsare da sadarwa.

Hakanan wani shahararren mawaki na Kano, Dauda Rarara, aka ce an nada shi a matsayin babban daraktan wake-wake na kwamitin, yayin da aka ce an nada wani dan kamfanin shirya fina-finai naNollywood kuma wakili a majalisar wakilai ta Jihar Legas, Honorabul Desmond Elliot, a matsayin Sakataren yada labaran kwamitin.

Aka kuma ce, shugaban ma’aikata na gwamnan Jihar Imo kuma mai neman tsaya wa takarar gwamna a karkashin Jam’iyyar ta APC a Jihar ta Imo, Uche Ugwumba Nwosu, zai yi aiki a matsayin sakataren kwamitin.

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Dakta Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Alhaji Mamman Daura duk sune Ubannin kwamitin.

Wakilan tuntuba na kwamitin sune, M.T Mbu, Sanata Yerima Bakura, Sanata George Akume, Sanata Abdullahi Adamu, Sanata Ita Giwa, Honorabul Gudaji Kazaure, Hajiya Ireti, Alhaji Ismaila Isa Funtua da Sanata Abu Ibrahim.

Advertisement
Click to comment

labarai