Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ma’aikacin Kwastan Ya Kashe Abokan Aikinsa Biyu

Published

on

A ranar asabar ne hukumar kwastam ta rasa ma’aikatanta guda biyu a wani hatsari na ban tausayi wanda ya faru a babban titin Badagry na jihar Legas.

Majiyanmu ta tabbatar mana da cewa marigayan sun hadu da ajalinsu ne yayin da suke cikin mota kiran Toyota Camry mai lamba kamar haka YLA 121 BJ,  a wajen shingen bincike lokacin da abokin aikinsu ya zo a cikin mota kiran Toyota Abalon mai lamba YAB 366 JY  ya murkushesu.

Dukkan su ma’aikatan guda uku suna bada rahoton aikinsu ne a boda guda daya  mai suna Same border command na jihar Legas.

Yayin da su  wadannan jami’an kwastam guda biyu wanda aka murgushe suka mutu nan take, shi kuma wanda yake tuka matan Abolon yana cikin mawuyacin hali inda ake amsar magani a babban asibitin Badagry.

Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, jami’in hukumar kiyaye hadarruka wanda ye ke kula da garin Badagry mai suna Fatai Bakare ya ce sun ajiye matattun a asibiti.

Shaidu sun ce hadarin ya faru ne a sanadiyyan fashewar taya.

Ya ce hadarin ya faru da misalin karfe 7 da minti 45 na safiyar asabar a wajen shinge bincike na Gbaji.

Ma’aikatan kwastam an murkushesu har lahira ne da matan Toyota Abalon wanda wani abokin aikinsu kwastam yake tukawa.

Matarsa ta sauko a kan gadan Gbaji lokacin da tayan matan ya yi bindiga. Sai ya kasa kulawa da ita sa’annan sai ya kasha wadannan ma’aikata.

Shi kuma kwamandan dake kula da yankin Bakare ya ce, wannan hatsari ya faru ne a sanadiyyan  mugun gudu.

Ya kara da cewa ma’aikatan kwastam suna cikin matansu a shingin bincikan na titi mai suna Lagos-Same Road sai dareban matan Abalon ya zo a guje ya murkushesu nan take suka mutu shi kuma wanda ya jawo hadarin yana cikin mawuyacin hadi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastam dake Same Saidu Abdulahi ya babbatar da aukuwan hadarin inda ya gano suna yan su wato Usman da Kabiru. Ya kuma tabbatar da cewa matukin matan Abalon jami’in kwastam ne mai suna George.

Ya kara da cewa a ranar asabar 14 ga watan Yuli na shekara ta 2018, ya samu rahotan faruwan hadarin wanda ya shafi jami’an kwastam guda uku na karamar hukumar Same dake  shingen binciken Gbaji.

Usman da Kabiru suna cikin wannan hadari na motan da ya yi sanadiyan mutuwarsu. Shi kuma dareban dayan matan mai suna George, yana kwance a asibiti.

A ranar asabar ne Diktan babban asibitin garin Badagry ya ce, direban motan Abalon yana cikin mawuyacin hali amma ana kula da shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: