Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Gidan Sama Hawa Hudu Ya Ruguje A Jihar Anambra

Published

on

Gidan sama mai hawa hudu wanda kamfanin Owelle-Aja ta gina a garin Obosi da ke cikin karamar hujumar Idemili a jihar Anambra, ya rushe a jiya da safe. Ginin ya rushe ne da misalign karfe 7 na safe kafin ma’aikatan da suke aiki a wajen su kai ga zuwa. A cewar mazauna yan kin,  ainihin ginin hawa biyu ne kafin mai gidan ya yanke shawarar kara hawa biyu kafin ya zo ya rushe saboda rashin kari.

Ya ce “matane suna gini mai tsawo a wannan wuri,  a nan kuma gini hawa biyu ai kauyanci ne, bayan an bar gini cikin ruwa ga kuma rana tana dukan sa har na tsawan shekaru, wannan kadin ya isa gini ya rasa karfi.”

Shugaban kungiyar Landlords Association Cif Chuka Chukwudebelu ya ce ruguje war ginin bai da alaka da rashin kyau kayan aiki sai dai gaskiyar al’amari shi ne ginin ya dade da aka yi watsi da shi sai daga baya kuma aka ci gaba da gini. Ya kara da cewa shi wannan mai gini bai yi saurin gama aikin ba watakila rashin isassun kudi ne.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: