Hazard Ya Amince Da Komawa Real Madrid — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Hazard Ya Amince Da Komawa Real Madrid

Published

on


Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard ya amince da albashin da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta bashi a kokarin da yakeyi na komawa kungiyar.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai ta bayyana Hazard a matsayin wanda zai maye mata gurbin Cristiano Ronaldo wanda yabar kungiyar a satin daya gabata zuwa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus.
Real Madrid dai tun da farko ta bayyana dan wasa Neymar a matsayin wanda zai maye mata gurbin Ronaldo sannan kuma ta tuntubi dan wasa Mbappe amma daga baya PSG ta bayyana mata cewa ‘yan wasannin nata guda biyu bana siyarwa bane.
Daman dai Hazard ya bayyana cewa yanason bugawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wasa anan gaba amma kuma labarai sun bayyana cewa tuni dan wasan ya amince da albashin da Real Madrid zasu bashi.
Sai dai har yanzu kungiyoyin biyu basu amince da cinikin dan wasan ba bayan da Real Madrid ta taya dan wasan fam miliyan 107 Chelsea kuma tayi fatali da tayin sai dai ana zaton Real Madrid za ta sake komawa da sabon tayin kudi.
Real Madrid dai ta shirya sake kai tayin kudi sai dai tuni Chelsea ta bayyana mata cewa idan tayin kudin yayi kasa da fam miliyan 175 baza ta siyar ba saboda tanason dan wasan yakasance dan wasa na biyu a wadanda sukafi tsada bayan Neymar.
Shima mai tsaron ragar kungiyar ta Chelsea, Thibaut Courtois ya bayyana aniyarsa ta komawa Real Madrid akan kudi fam miliyan 31.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!