Manchester United Za Ta Bayar Da Damian Domin Karbar Perisic — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Manchester United Za Ta Bayar Da Damian Domin Karbar Perisic

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara tunanin bada dan wasanta na baya, Matteo Damian dan kasar Italiya domin karbar dan wasa Iban Perisic dan kungiyar Inter Millan kuma dan kasar Crotia wanda kungiyar tafasa siya a shekarar da ta gabata.
A shekarar da ta gabata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kusa siyan dan wasan mai shekaru 29 a duniya wanda tauraruwarsa ta haska a gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Rasha.
Bayan tauraruwar dan wasan ta haska a kasar Rasha mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kaf ata Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana aniyarsa ta sake neman dan wasan wanda a ka yi wa kudi fam miliyan 50.
Perisic wanda ya sake sabon kwantaragi a kakar da ta gabata ya bayyana cewa yanason cigaba da zama a kungiyar tasa bayan daya taimakawa kungiyar ta samu tikitin gasar cin kofin zakarun turai a kakar wasa mai zuwa.
Manchester United dai tana zawarcin dan wasan sai dai tanason ta bada dan wasanta na baya, Matteo Damian, wanda Inter Millan din take nema domin kara karfin baya.
Damian dai yanason komawa kasarsa ta haihuwa Italiya domin cigaba da buga wasa sakamakon baya samun buga wasanni akai-akai bayan daya buga wasanni 8 kacal a kakar da ta gabata kuma United din ta kare kakar wasan a matsayi na biyu.
Perisic dai ya zura kwallaye 11 sannan ya taimaka an zura kwallaye 9 a kakar wasan da ta gabata a kungiyar ta Inter Millan.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!