Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Shugaban Kungiyar Asiri Yana Kokarin Shigar Da Yara ‘Yan Sakandire A Inugu

Published

on

‘Yan sandar jihar inugu sun kama ‘yan kungiyar asiri mutum biyu saboda suna zarginsu da shigar da yara maza da mata’yan sakandire a cikin kungiyan.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan SP Ebere Amaraizu ya ce, an samu wannan nassaran ne a wani  bincike da rundunar hadin gwaiwa mai suna Anti-Cultism ta gudanar.

Amaraizu ya kara da cewa wadanda ake zargi sune Emmanuel Onuh dan shekara 18 da kuma Chukwuebuka Egwu dan shekara 19 da haihuwa. Ya ci gaba da cewa matsafan sun tsunduma a cikin wannan aikin wanda ya ke da alaka da manyan laifuka shekaru da dama kafin rundunar hadin gwaiwa na Anti-Cultism su samu nasarar cifke su.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan ya ce su wadanda ake zargi, a baya kungiya ce da suke yima mata  ‘yan sakandire fyade kafi su rikida su koma kungiyan asiri mai suna White Angels Cult.

Amaraizu ya kara da cewa ita wannan kungiya mai suna White Angels Cult sun samu goyan baya daga matan T-stars da Ayez confraternities.

Ya kuma ce daya daga cikin wadanda ake zargi wato Onuh, ya bayyana mana cewa shi mai gyaran fanfu ne kuma yana tare da ‘yar’uwarsa a layin Mount, dan asalin karamar hukumar Nkanu ta gabas a jihar inugu kuma shi ne mai gudanarwa na kungiyar T-Star confraternity ta jihar.

Ya ce Onuh ya shiga kungiyar asiri ne tun a shekara ta 2015 lokacin da ya ke SSS I a sakandire cikin jihar Inugu da suna Withheld sai ya bara zama a cikin daji bayan makarantarsu.

“Ni shiga wannan kungiya na asiri ne ta hannun abokina tare da mun alkawarin cewa zai bani kariya idan wata matsa ta same ni, shi ya sa na shahara a cikin jama’a ya zama koda yaushe ina tare da mata amma yanzu na yi ladaman abin da

na yi”, mai magana da yawun ‘yan sanda ya rubuta abin da Onuh ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa ‘yar makarantar sakandire na karshe da Onuh ya shigar cikin kungiyan it ace Oliber wanda aka fi sani da Chaplet, wanda kwadasta matan ya ke saba kawo masu idan an tashi daga makaranta.

Ana shi daya bangaran kuma na kungiyan asirin mai suna Egwu wanda aka fi sani da makashi, ma’ajin kungiyar T-Star confraternity, kuma dan bangaran kabilar Amoli Awgu shima yana zaune ne a layin Mount da ke hihar Inugu.

Amaraizu ya ce, Egwu ya shiga wannan kungiya ne tun a shekara 2014 lokacin da ya ke JSS III a makaranta cikin jihar kafin daga baya ya bar makarantar ya hadu da Emmanuel Onuh su ci gaba da aikin kungiyan.

Ya kara da cewa Egwu yana sha’awan matan  makarantar sakandire wannan ya bashi daman shigar da ‘yan matan cikin kungiyar mai suna White Angels Cult.

Ya ce za su yi cikakken bincike aka lamarin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: