Za A Yi Canje Tsakanin Lukaku Da Bale — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Za A Yi Canje Tsakanin Lukaku Da Bale

Published

on


Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyoyin Real Madrid da Manchester United suna shirin musayar ‘yan wasan kungiyar yayinda ake rade radin Bale zai koma Manchester United sai Lukaku yakoma Real Madrid.
Manchester United dai ta dade tana zawarcin dan wasa Gareth Bale wanda ya koma Real Madrid daga Tottenham sai dai dan wasan yanason tattaunawa da sabon kociyan Real Madrid kafin ya bayyana makomarsa na zama a kungiyar ko kuma tafiya.
Dan wasa Lukaku dai ya buga gasar cin kofin duniya kuma tauraruwarsa ta haska yadda yakamata bayan daya zura kwallaye hudu cikin wasannin daya buga wanda hakan yaja hankalin kungiyar Real Madrid wadda daman take neman dan wasan gaba.
Real Madrid dai za ta daina neman mai tsaron ragar Manchester United, Dabid De Gea, idan har ta samu daukar Lukaku bayan da ta kusa cimma yarjejeniya da mai tsaron ragar Chelsea, Thibaut Courtois wanda ya bayyana aniyarsa ta komawa Real Madrid .
Sai dai mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ya bayyana cewa ba zai yadda ya siyar da Lukaku ba ko da kuwa zai rasa damar siyan Gareth Bale wanda ya dade yana nema.
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen dai itama tana zawarcin Bale wanda take ganin zai maye mata gurbin Frank Ribery ko kuma Arjen Robben wadanda girma ya kamasu a kungiyar.

Advertisement
Click to comment

labarai