Alamu Sun Nuna APC Za Ta Sake Samun Nasara A Zaben 2019 –Hon. Bashir Wada — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Alamu Sun Nuna APC Za Ta Sake Samun Nasara A Zaben 2019 –Hon. Bashir Wada

Published

on


An bayyana cewa, daga dukkan alamu jam’iyya mai mulki ta APC ce za ata sake kafa mulki a dukkan matakan gudanar da mulki na kasar nan a zabukan da za a gudanar a shekarar 2019, wannan bayanin ya fito ne daga bakin dan takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar karamar hukumar ta Nassarawa Hon. Bashir Wada, a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya a Kano ciki harda jaridar Leadership A Yau.
Ya kara da cewa, al’ummar karamar hukumar Nasarawa dake jihar Kano ne musamman ‘yan siyasa tare da ‘yan uwa da abokan arziki har da ‘yan kasuwa suka yanke shawar cewa ya fito takarar dan majalisar wakilai ta tarayya a tutar jamiyyar APC a zaben da za a gudanar a 2019.
Dan siyasan sannan kuma dan kasuwa dake gudanar da harkokn kasuwancinsa a unguwar ‘Yankaba, da kwanar Singa, ya ce, idan Allah ya sa ya samu nasara zai dora a kan yadda ya saba taimakawa al’umma marasa karfi dake yankin ta karamar hukumar da suka hada da ilimi mai inganci ga maza da mata .
Dan takaran ya ce, bayan samar da ilimi harkokin lafiya da koyar da sana’oin dogaro da kai shima na daya daga cikin abin da zai ba shi muhimmancin gaske. Bashir Wada, ya kara da cewa ya zabi fitowa a jam’iyyar APC ne sakamakon kara samun magoya baya da take da shi a jihohin kasar nan sannan kuma tana kwatanta gaskiya da adalci kamar yadda jam’iyyar ta gudanar da zaben shugabancin ta kwanaki.
Ya kuma ba da misali ga zaben gwamnan jihar Ekiti da aka kammala kwannannan ya nuna inda jam’iyyar APC ta samu galaba hakan ya na cewa a zaben da za a gudanar 2019 za ta sake kafa gwamnati a jihar Kano da kasa baki daya da yardar Allah inji shi.
Daga nan sai ya yi kira ga daukacin ‘yan jam’iyyar ta APC na karamar hukumar ta Nassarawa da jihar Kano dasu tabbatar sun zabi mutanen da suka cancanta musamman wadanda zasu kawo masu ci gaban rayuwarsu.Sannan har ila yau su tabbatar sun je hukumar zabe domin karbar katin zabe domin sai da shi ne ake zaben shugabannin da zasu kawo musu canjin da ake bukata.
Bashir Wada ya yi amfani da wannan dama da yaba wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, game da yadda yake gudanar da aikace aikace ga al’ummar jihar, sai ya shawarce su da sake zaben shi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2019 domin sune suka fi cancanta.
Da fatan Allah ya kara bai wa jihar Kano da kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!