An Bukaci Gwamnatin Filato Da Ta Tarayya Da Su Gyara Kasuwar Jos Da Ta Kone — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Bukaci Gwamnatin Filato Da Ta Tarayya Da Su Gyara Kasuwar Jos Da Ta Kone

Published

on


An nemi gwamnatin Tarayya da ta jihar Filato da su yi amfani da kasafin ku din wannan shekara wajen sake ginin babbar kasuwar Jos da ta kone don bun kasa harkokin kasuwnaci da inganta tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na kasa, reshen jihar Filato Usman Dafaan ne yayi wannan a zantawar da yayi da yan jarida bayan a Jos jmkadan bayan anrantsardasu akwanakin da suka gabata, ya ce konewar kasuwar ya sanya yan kasuwan cikin mawuyacin hali, a sanadiyar rashin ingantaccen wurin da zasu zuba kayayyakinsu sugudanarda harkokin kasuwanci.
Ya ce sake gina kasuwar zai maido da zamanlafiya da janyo hakalin masu zauba jari so zo jihar suzuba jarinsu.
Ya yaba wa Gwamnan jihar Barista Simon Bako Lalong bisa ko karin da ya ke yi na ha da kan al’ummar jihar kuma ya nemi al’ummar jihar da su ba shi kyakkyawan ha din kai da goyon baya don ya sami kwarin gwiwar gudanar da harkokin mulkin jihar cikin kasar.
Daga cikin sabbin shugabannin da aka za ba su tafiyar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru hu du masu zuwa sun ha da da Usman Daffaan shugaba, mista Syel banus S. Membas mataimakin shugaba, Honarabul Terry Y. Da bou mataimakin shugaba na biu, sai kuma Alhaji Sabo Adamu a ka za be shi Sakataren kungiyar.
Sauran wa danda aka za ba a za ben da aka gudanar sun ha da da Yusufu Audu wanda ya sami mukamin Ma’ajin kungiyar da Laldip Demkur da aka bashi Sekataren ku di bi-da-bi.
Sauran kuma su ne: Morice mataimakin Sakatare, Mista Mathew Baba Guyel mai bibnciken kudina 1, da mista Daniel Yemkiling mai binciken dudi na 2, Aliyu Abubakar jami’in hulda da jama’a, Boddi Dakor Dede Sakataren Tsare Tsare, sai miss Ginka Ungwunyi wanda ta sami mukamin mataimakiyar sakataren tsare-tsare.

Advertisement
Click to comment

labarai