Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Yi Garkuwa Da Basarake An Kuma Kashe Dansa A Jihar Kogi

Published

on

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken garin Jakura na cikin karamar hukumar Lokoja a jihar Kogi mai suna Cif Usman Ajibola tare da kasha dansa mai suna Rufai Ajibola.
Mai magana da yawun ‘yan sanda mai suna Mista William Ayah ya tabbatar da aukuwan lamarin. An yi garkuwa da basaraken ne lokacin da suke dawowa daga garin Oworo sai masu garkuwa da mutane suka farmake su a tsakanin kauyen Imo da Igbonla kilomita 15 tsakanin su da garin Jakura.
Su biyar ne aka sace ciki har da direbansa, sai dai nan da ke suka kasha dansa har lahira tare da garkuwa uban.
‘Yan sanda sun ce suna binciken lamarin. A halin yanzu, gawar Rufai an ijiyeta a dakin ajiye gawa na garin Lokoja.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: