Majalisar Dinkin Duniya Da Kasar Japan Sun Kaddamar Da Shirin Taimakawa Mata Da Yara Da Rikicin Boko Haram Ya Shafa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Majalisar Dinkin Duniya Da Kasar Japan Sun Kaddamar Da Shirin Taimakawa Mata Da Yara Da Rikicin Boko Haram Ya Shafa

Published

on


Ha din gwiwar Majalisar Dinkin Duniya da kasar Japan sun kaddamar da wani shiri na taimakawa Mata da Kananan Yara wa danda rikicin Boko Haram ya ta gaiyara a Arewa-masu Gabashin Nijeriya.
Shirin wanda aka fara gwada shi a ranar Asabar din da ta gabata a jihar Barno ya mai da hankali ne wajen samarwa da Matan aikin yi da kuma koya musu sana’o’i don su dogara da kan su, su farfa do daga halin da ‘yan Boko Haram suka sa su a shekaraTara da ta gabata.
Sannan kuma shirin zai karewa Matan mutumcin su.
Taron dai wa danda ya samu halartan din bin mutane, wakilan kasa da kasa, Shugabannin Kungiyoyi, wakilan ‘Yan jarida daga Jihohi daban-daban, sai kuma sauran din bin Al’umma da dama.
Daya daga cikin ‘yan gudun Hijiran wace ‘yan Boko Haram suka kashe mata mijin da yanzu ta ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira na Maiduguri tare da ‘ya ‘yanta guda Bakwai Malama Hafsat Mohammad ta amfana da shirin.
Ta bayyana mutukar farin cikinta da abin da ta koya, ta ce; “zan yi amfani da wannan abun da na koya da kuma tallafin da na samu wajen dogoro da kaina, zan bude Shago, na kula da kaina da kuma yarana”.
Ministan walwala da jin dadin mata, Ifeoma Anagbobu, ta bayyana cewa yana da matukar mahimmanci a ba mata goyon baya wajen yadda za su iya dogaro da kansu,musammamma kayan da ake nemansu a kasuwa, Ta wanan bangare ne za a iya shawo kansu ta yadda
Hakan zai hana matan fadawa wani mawuyacin hali.
Shi ma da yake jawabi a wurin taron Ambasadon Kasar Japan a Nijeriya Mista Yutaka Kikuta, ya shawarci matan da su yi amfani da abun da suka samu wajen inganta rayuwar su, dan ya zama suna tafiya kafa da da kafa da da ‘yan uwan su Maza.
Kuma ya tabbatar musu da cewa Kasar Japan za ta ci gaba da taimakon matan Nijeriya tare da ha din kwiwar Majalisar dinkin Duniya.
Wakiliyar Majalisar dinkin Duniya da kungiyar ECOWAS mai kula da bangaren Mata Comfort Lamptey ta ce za su ci gaba da aiki da Nijeriya wajen daidaita tsakanin Maza da Mata batare da tauye ma Matan ha k ki ba, kuma za mu mayar da hankali wajen taimaka ma mata a Nijeriya musamman bangaren da ‘yan Boko Haram suka rabasu da mazajensu da muhallinsu ..
Ta kara da cewa; ”taron nan namu na yau ya nuna yadda Mata lallai za su iya dogaro da kansu, saboda yadda suka nuna abun da aka koya musu a aika ce, don haka in aka ci gaba da koyawa Matan wa dannan sana’o’in, to lallai ba karamin natija za a samu ba”.

Advertisement
Click to comment

labarai