‘Asirin Fayose Ya Tonu’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASIKU

‘Asirin Fayose Ya Tonu’

Published

on


Salam, Editan LEADERSHIP A YAU JUMA’A, ina so ka bani dama na bayyana irin nawa ra’ayin game da Fayose, Gwamnan Jihar Ekiti mai barin gado. Tun daga lokacin da jam’iyyar APC ta ci nasara a zaven da ya gudana, Gwamna Fayose sai ya shiga wasanbuya saboda Hukumar EFCC tana shirin cafke shi, bisa zarginsa da laifin karkatar da biliyoyin naira.
Gwamnan tun daga lokacin da ya buya, cikin sirri sai ya sa aka nema masa tikitin jirgi domin ya tsere dagakasar Nijeriya zuwa jamhuriyarkasar Benin daga nan kuma zuwakasar Faransa. To dama tun daga lokacin da ya shiga wasanbuya shi da jami’an tsaronkasar nan suke bin diddiginsa da duk wani motsinsa, kuma hakan ne ya kai su ga nasarar bankaxo wannan yunquri na shirin tserewa da Fayose ya yi domin ya tsallakewa tarkon hukumar EFCC..
Tabbas Baba Buhari yana aiki, babu shakka marasa gaskiya kun shiga uku akasar nan. Allah Ka taimaki gwamnatin Buhari, Ka ba shi nasarar kawokarshen badaqalar da wasu ke tafkawau.
Saqo daga Muhammad Idris (Babanne), Abuja.
07065279510

•Yaushe Za A Kawokarshan Zubar Da Jinnin Al’umma
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. Haqiqa mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke manakaiqayi a rai tare da isar da saqon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummarkasa. Muna muku addu’ar Allah yakara muku hikima da basirar aiki da kuma bunqasar wannan jarida mai farin jinni bakidaya.
Edita barka dakoqari, ina fatan za ka isar min da roqona cikin hawaye ga gwamnatin taraiyya da na jihohinkasar nan, su hanzarta yin dukkan mai yiwuwa domin kawo karshen zubar da jinin al’umma a dukkan sassankasarnan. Domin irin wannanketare iyaka ba zai tava haifarwa dukkasar da irin wannan ke wakanada mai Ido ba. Su kuma masu yin zagonkasa ga lamuran da suka shafi tsaron rayuka da dukiyar al’umma da sauran fannoni su ji tsoron Allah su daina, domin suna cin amanar mahaliccinsu ne, wanda a cikin hakan babu riba sai mummunar faxuwa. Allah ka ganar damu, amin.
Saqo daga Dahiru Dauda (KGY) Bindawa.
08030693021

•Atiku Mai Abun Mamaki
Assalamu alaikum,LEADERSHIP A YAU JUMA’A, ina so ku bani dama na faxi damuwata a kan tsohon mataimakin shugabankasa Alhaji Atiku Abubakar.
A Nijeriya akwai waxanda idan aka buxe badaqalar cin hanci da rashawarsu,kwaqwalwar mutane zai sha wahala kafin ya iyadauka.
Atiku ya ce babu gwamnatin da ta kai ta shugabankasa Muhammadu Buhari cin hanci da rashawa, gwamnatin da aka kafa da hannun sa ciki.
Na kasa fahimtar me Atiku ya ke nufi. Idan yana nufin cin hanci da rashawa, saboda a dunkule ma’anar rashawa shi ne Gwamnatin Obasanjo da Atikukarkashin mulkin PDP a shekaru 8. Duk wani ma’ana in dai a Nijeriya ne zai biyo bayan wannan.
Atiku zai iya kamfe yanda yake so, amma kar ya zagi tunaninmu da fahimtarmu, ta hanyar yaudaran kansa cewa zamu tava kallon shi a matsayin wani abu banda kasurgumin jakadan cin hanci da rashawa.
Babu shakka akwai cin hanci mai gudana akarqashin gwamnatin APC a yanzu, amma ko kaxan bai yi kama da gwamnatin PDP na su Atiku ba. Muna buqatan canji don har yanzu APC akwai matsala, amma ba zamu tava canzawa mu koma gidan shekaran jiya ba. Da babu gara ba daxi.
Saqo daga Mahmud Isa, Yola.
08106792663

•Buhari Aheri Ne Ga Mutanen Arewa
Assalamu alaikum, LEADERSHIP A YAU JUMA’A. haqiqa mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke manakaiqayi a rai tare da isar da saqon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummarkasa. Muna muku addu’ar Allah yakara muku hikima da basirar aiki da kuma bunqasar wannan jarida mai farin jinni bakidaya.
Raddi ga mutanen da ke bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya kasa yiwa yankin Arewa kowanne irin aiki, zan bayyana wasu ayyukan da ake gabatarwa yanzu haka a yankin Arewacin Nijeriya.

•Iskar Gas Zuwa Arewa
Gwamnatin shugaba Buhari ta bayar da kwangilar aikin kawo iskar Gas zuwa yankin Arewa a kan makudan kuxaxe har sama da dollar biliyan Biyu, kuxaxen da suka haura naira tiriliyandaya, an raba aikin zuwa kaso uku ta yadda za a yi saurin kawoshi zuwa Arewa.
– Ajaokuta zuwa Abuja.
– Abuja zuwa Kaduna.
– Kaduna zuwa kano.
Aiki ya yi nisa yanzu haka, ana fatan za a kammala cikin dankanqanin lokacin da aka tsara.

•Samar Da Hasken Lantarki A Damdin Mambila
Duk dai akoqarin gwamnatin shugaba buhari na inganta tattalin arzikin yankin Arewa, hakan ya sa ya ware makudan kuxaxen da yawansu ya haura naira tiriliyan biyu ga aikin samar da hasken lantarki daga Damdin Mambila wanda ke yankin Arewa, aiki ya yi nisa ana sa ran kammalawa kamar yadda aka tsara nan gaba kaxan. Akwai wasu ayyukan lantarkin da ake yi a wasu Dama daman dake Arewa da kuma masu amfami da iska ko rana. Waxanda suma aka ware musu makudan kuxaxe.
– Zungeru.
– Daxin kowa.
– Windmills turbine a katsina.
– Manyan tarasfoma guda goma masukarfin 40mw.
– An ware za a kashe sama da biliyan 200 domin janyo wuta ta manyan turakun dakon wutar lantarki daga manyan tashoshi samar da wuta , zuwa tashoshin raba su dake Arewa.

•Binciko Man Fetur Arewa
Daga zuwan shugaba Buhari mulki zuwa yanzu ya kashe makudan kuxaxen da suka haura naira biliyan tamanin abangaren nemowa yankin Arewa man feturdin da suma za su dogara da kansu, kuma a dena yimusu gori, Alhamdulillah zuwa yanzu an samo Fetur a yankunan Arewa masu yawa, Bauchi, Gombe, Taraba da sauran yankunan da ake ci gaba da aiki yanzu haka.

•Samar Da Tsaro A Arewa
A kwanakin baya kaxan lokacin da shugaba Buhari ya ziyarcikasar Amurka, ya sanya hannun siyo manyan jiragen yaqi tare da kayan yaqi na sama da naira Biliyandari biyu duk dai saboda yankin Arewa ya samu zaman lafiyar da al’umma za su samu damar gudanar da al’amurasu cikin nutsuwa.
Qaunar da shugaba Buhari ke yiwa yankin Arewa ya sanya yake gudanar da ayyukan da za su temaki yankin.
Saqo daga Isma’il Yusuf, Kagarko.
08168499372

•Nasaran Shugaba Buhari
Salam, LEADERSHIP A YAU JUMA’A, don Allah ku bani dama in faxi irin nawa ra’ayin a kan nasaran da shugabankasa ya samu.
Kafin zuwan Shugaba Muhammadu Buhari kan kujerar mulkin Nijeriya a shekarar 2015, kusan dukkan manyan kamfanonin dake samarwa dakasarmu kuxaxen shiga sun dena aiki, yayin da aka haxa kai aka siyar da wasu duk don a ji daxin kara tatse arzikinkasar.

Misali:
-Babban Kamfanin Ajakuta Steel tuni har sun sayar da shi maimakon su yikoqarin gyarawa, ga kuma makudan kuxaxen suka ware da sunan za su gyara kamfanin.
Yanzu kuwa bayan zuwan Buhari cinikin da aka yi an tayar da shi, har shugaba Buhari ya bayar da manyan kuxaxen da aka sake gyara shi har yana ci gaba da aiki yanzu haka.
-Matatan maidin dake Nijeriya kusan dukkan su ba sa aiki, suna sane suka lalata su ta yadda za su samu damar sayarwa kansu da su gabadaya, har sun fara shirye -shiryen siyar da su, amma bayan da Shugaba Buhari ya zo tuni an gyarasu sun ci gaba da aikin da yake samar da man feturdin da muke amfani da shi akasar.
– Titunan jiragenkasan dake Nijeriya duk sun lalace, jiragenkasan suma sun lalace ba sa iya gudanar da aikin daya kamata, suna sane suka lalata kamfamin. Domin suki biyan ma’aikata albashi.
Amma tun bayan zuwan shugaba Buhari sai gashi cikin shekara uku kacal har an dawo da martabar zirga-zirgar jiragenkasa cikin mutumci kamar yadda ake yi akasashen duniya.
A hankali cikin nutsuwa shugaba Buhari yake samar da ayyukan alheri a Nijeriya, wanda ina da yaqinin idan ya sake samun damar ci gaba da mulkinmu kafin shekarar 2022 za a ga abun mamakin da zaidaga darajar Nijeriya a idanun duniya, kuma rayuwa mai sauqi tare da inganci za ta bayyana a zahiri a wajen dukkan al’umma.
Saqo daga Usman Hamisu, Kaduna.
08160874213

Advertisement
Click to comment

labarai