Ko Yau Aka Yi Zave, Ni Zan Lashe Mazavar Kusada – Hon. Amin — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

TATTAUNAWA

Ko Yau Aka Yi Zave, Ni Zan Lashe Mazavar Kusada – Hon. Amin

Published

on


ALHAJI AMINU ABASHE, fitaccendan siyasa ne akaramar hukumar Kusada dake jihar katsina, wanda yanzu kumadan takarar Majalisar wakilai ne ta jihar Katsina, ya ce, ba shi da burin da wuce ya taimakawa talakawa ‘yan uwansa. Alhaji Aminu ya bayyana haka a tattaunawarsu da wakilan LEADERSHIP A Yau Juma’a, IDRIS ALIYU DAUDAWA DA RABI’U ALI INDABAWA yayin da ya kai ziyara ofishin. Ga yadda hirar ta kasance
Masu karatu za su so sanin cikakken sunanka?
Sunana Aminu Abashe na fito daga garinn Yashenkaramar Hukumar Kusada ta jihar Katsina.

To Malam Aminu kaidan kasuwa ne kumadan kwangila me ya baka sha’awa ka shiga harkokin siyasa?
Abin da ya sa na shiga harkar siyasa shi ne saboda wani lokaci sai ta harkar siyasa ce, za ka iya taimakon mutane amma idan kana da niyyar yin taimakon, saboda akwai taimakon da zaka iya yi, idan Allah ya hore maka arziki da kuma, akwai kuma taimakon da ba zaka iya yi ba sai akan cikin gwamnati, hanyar da kuma zaka niya shiga gwamnati a yanzu, ita ce ta hanayar ga shiga siyasa, ta nan ce zaka shiga gwamnati ka taimakawa jama’arka wajen amso masu hakkokinsu. Irin waxanda suka maqale ka tabbatar da ka amso masu su, inda zaka samar masu wakilci domin ganin cewar su ma ba’a barsu a baya ba. Wannan shin ne dalilin da yasa na shiga siyasa da domin ka bani wani abu ba ko kuma kwaxayin matsayi,wannan shine babban dalilin da yasa na shiga siyasa saboda na taimaki al’umma ta.

A wacce jam’iyya kake shirin fitowa ita wannan takara?
Duk wanda ya sanni ya san ni a jam’iyyar adawa, ma’ana anan it ace tun da aka dawo harkar siyasa dagan gadan, ni ban tava zama a jam’iyyar data kafa gwamnati ba, sai wannan karon da APC ta kafa gwamnati, to bayan ta kafa gwamnati, abubuwan da muka yi ta gaya ma mutane, na cewar jam’iyyar adawa da muke cikinta, jam’iyya ce mai adalci. Zata taimaki mutane zata yi masu ayyuka, tosai bayan data kafa gwamnati ne, sai muka ga duk abubuwan da muka faxawa mutane sun zamanto ba gaskiya bane, kamar ni nan da nake dagakaramar hukumar kusada ba wani abinda zan iya nunawa ince yau an taimaki itakaramar hukumar, ko kuma al’ummata da wasu ayyuka waxanda ba waxanda gwamnatin data gabata tayi ba. Saboda haka shi yasa nake ganin ita jam’iyyar da muka bi baya, har muna faxinwasu maganganu dangane da ita, waxanda wasu basu bma dace ba, ko su macuta ne. sai muka gane abindaya ne, sai muka koma muka shiga jam’iyyar PDP wadda ake ganin akwai waxansu abubuwan data yiu,waxanda wasu mutane basu jin daxinsu ba. Shi yasa muke ganin tunda akwai wasu mutane da suke ganin mutuncinmu, yasa muka koma jam’iyyar PDP saboda ba ita jam’iyyar ce ba mutanen , amma su mutanen ai sune ita hjam’iyyar. Wani abu kuma wanda yake daban ne ko APGA mutum yake idan dai dama can shi mutumin kirki ne, to haka yake, ko wacce jam’iyya ya koma, shi yasa zan yi takara a cikin PDP.

Ya kake ganindan majalisa mai wakiltarkaramar hukumarku ke gudanar da mulkinsa?
Gaskiya ce muna da wakili kumakaramar hukumar ta yi sa’a saboda ga shi har speaker ya fito daga cikin ta, amma kuma inda muka yi rashin sa’a shi ne, shi a matsayin shi na wakilin jama’a , ya zubar da wannan dama wadda Allah ya bashi, saboda bai yi amfani da damar da Allah ya bashi ba, domin ya kasance kujerarshi bata yi ma karamar hukumar amfani ba, dalili kuwa shi ne da Allah ya bashi wannna dama , sai ya jawo daga abokan shi, sai ‘yanuwanshi su kaxai yake ma’amala dasu a cikin siyasar da ake ciki. Saboda ita gwamnati ta fikarfin kace daga ‘yanuwanka sai abokanka za ka yi tafiya dasu, duk wata kujera ta siyasa kace daga su ba wanda zaka iya tafiya dashi. Wannan ita ce babbar matsalar da ya samu wadda kuma ta sa duk wanda ya zave shi, bai jin daxi saboda ba wani abin da zai nuna wanda zai ce a dalilin wannan kujera ta shi ta shugaban majalisar dokoki ta Katsina.

To kafin ka koma jam’iyyar PDP ba ku yi zama da Shugabannin jam’iyyar APC nakaramar hukumarku ba?
To da ka yi zave gani suke yi da mu da babu dukdaya ne, tun wajen fitar dadan takara muka ga cewar irinmi irinmu, da mutumin da zamu marawa baya shi ne marigayi Sanata Kanti Bello Allah ya jikan shi da gafara amin. Tun daga wancan lokacin ne muke ta samun savani , suna yi mana ganin kamar mu maqiyankaramar hukumar kusada ne. Ba mu yin abubuwan da suka ce suna so, kuma mu abinda muka fahimta dangane da fitar dadan takara na cikin gida wannan ra’ayi ne, akandoradan takara bisa ma’auni ka yi tunanin cewar wannan shi ne idan ka zave shi zai iyakyautawa al’umma, wannan shi ne dalilin da yasa muka zavi Kanti Bello, da muka zo kuma kan maganar wakilindan majalisar tarayya shi bai isa ya ce, bamu muka yi ba wato Ahmed Babba Kaita mai wakiltar mazavar Kusada da Ingawa bai isa yace bamu muka yi shi ba.

Su waye iyayen gidanka a siyasa
Ina da iyayen gida na siyasa saboda lokacin da na shigo jam’iyyar PDP na san cewar tana da manya a cikinta, saboda haka dana shigo ni ban rena sub a, na maida su sune iyayen gida na.

To wane kira za ka yi ga magoya bayanka, daga PDP ko APC, idan aka tsaida kai takara?
Ni dai na sani a yanzu tafiyar da ake ciki, kuma jam’iyyara APC idan ana haihuwa za iya cewa da mu aka haife ta akaramar hukumar Kusada. Sabda haka yanzu haka, acikin jam’iyyar APC ina baka tabbacin, in yau aka yi zave ina da kashi 40 daga cikinta, waxanda suna APCdin za su zo su zave ni, banda ‘yan jam’iyyar PDP. Kamar yadda na gaya maka mutum ake dubawa yanzu, muna zaune lafiya da mutanen nan, kuma ba alfahari ba mun yi musu abinda za su san cewa mun yi musu.
Kuma badan jam’iyyar PDP ko APC, ko APGA kake, a matsayin da ake ciki in ka zo gidana ni ban banbanta ba, abinda nakedauka, dukdankaramar hukumar Kusadadan uwana ne, idan abu ya samudankaramar hukumar Kusada ko a wace jam’iyya kake ni ya same ni.
Zan yi iya bakinkoqarina in ga na taimaka maka, ko na cire ka daga cikin yanayin da ka shiga, sai dai in abin ya fikarfina.

APC ta kasu biyu kamar yadda PDP ma ta kasu haka, to a PDP wacce kake ciki?
To in ka lura ni abin da na sani PDP dai gudadaya na sani, nPDP yanzu ba maganarta ake ba, domin tana cikin APC. Saboda haka ni ban san wata nPDP ba, ko wata PDP can daban, abin da na sani na san jam’iyyar PDP gudadaya ce tak.

Amma rahotanni suna nuni da hakan…..
Gaskiya ne, abin da nake gaya maka shi ne, nPDP da kake magana har yanzu tana ciki APC. Sai dai alaqa da ake yi da ita ta wasu hanyoyi, amma dai a fito a matsayin jam’iyya ai PDP itadaya ce tak babu wata jam’iyya.

Shin akwai wani abu da za ka iya bayyana wa al’ummar mazavarka idan Allah ya baka wanna kujera?
Idan Allah ya kaimu ga nasara kamar yadda duk wanda ya sanni a fagen siyasa, kullum na kan yikoqari mutumin da na ga an zalunta na kare masa mutuncinsa, ba sai na fax aba, akwai abubuwa da yawa makamancin abubuwan da na yin a kare mutuncin mutane a inda na ga an zalunce su, kuma bai dace in fito in faxa in ce na yi kaxa, sai kuna iya bincikawa, kuma zan iya baku misalai kaxan na irin abubuwan da na kawo wa yankin namu cigaba.
Na fahimci cewa gwamnatin APC da ta zo akwai abubuwa da gaza, duk mutumin da ke jihar Katsina ya sani, kuma na godewa Allah cikin wannan hirar akwai bakatsinedan uwana, ya sani tun daga 1999 yara da iyayen yara ba su san biyan kuxin WAEC da NECO ba, amma an wayi gari da gwamnatin APC ta zo bata iya biyan wannan kuxaxe.
Ta wannan dalili ya sa yara sun zama daina zuwa makaranta, saboda sun gaza su yi jarabawar fita daga Sikandire, wasu daga nan karatun ya yanke. Da na fahimci wannan sai nag a wacw irin gudunmawa zan iya bayarawa, b azan iya cewa duk mutumin da kekaramar hukumar sai na biya masa kuxin makaranta, sai tun da muna mazavu 10 akaramar hukumata kowace mazava adauko mutum biyar-biyar ko wace mazava, inda akadauki mutum 50 na biya masu kuxin makaranta, na WAEC ko NECO, kuma duk wanda ya jekaramar hukumata zai san an yi wannan, kuma ya je makarantun da muke da su zai san an yi wannan. Kuma mutanen nan da na biya wa, da mutuwa da su ban san su ba, ‘yayan talakawa ne waxanda iyayensu ba za su iya biy masu kuxin makaranta ba, wannan kaxan daga ciki kenan.
Sannan in da muka samu matsalolin hanya da damina mutane ba sa iya bi, mu kan bi mu gyara dadan abinda Allah ya hore mana, da kuma marasa lafiya, wani z aka ga larurarsa kaxan ce, amma saboda yanayo na rayuwa da aka shiga ana ta kai, sai ka ga mutum ya bar larura a jikinsa ta fikarfinsa.
Akwai wani mutum da aka kawo bai da lafiya na tausaya masa, shekara kusandaya da wani abu an ce yana bahaya ta ciki, duk matsalar na kaxan ce in da an tare ta, amma an bar mutum gwamnati takyale shi maimakon ta nema masa lafiya ta gaza. Muka je mukadauke shi muka kai shi asibiti, aka yi masa aiki na biya har ya warke, yanzu yana nan yana rayuwarsa kamar yadda kowa yake yi.
To duka irin waxannan abubuwa idan na ce zan ta kaow maka su suna da yawa.

Shin za ka iya tuna wasu ayyuka da shi Sifika na yanzu yayi a wannankaramar hukuma?
Kamar yadda na sani babu wani aiki gudadaya da zan iya cewa ga shi wanda shi yayi shi, ko da na musamman ne a aljihunsa ko kuma wanda za a ce gwamnati ta kawo. Kuma wanda duk gwamnatin ta kawo na gansu a zahiri, wanda da su gara babu.

Kamar waxanne ayyuka ne?
Yawwa, a mazavata akwai wata hanya lokacin da muke kamfen, Masari mun shigakauyen da shi yayi musu alqawari cewa idan Allah ya ba shi gwamnati za su yi wannan hanya, daga garin Gidan mutumdaya, zauwa wani gari da ake kira Jeri, idan damina ta yi akwai rafi da ake cewa kwanta, da damina mutanen garin sai dinga kwayewa, wasu sai koma takasar Kankiya su shigokasarsu, saboda hanyar bata biyuwa.
To an kawo motoci za a yi aiki da zumma yaudara irin ta ‘yan siyasa, amma aikin nan ba yi ba, aka zo akadan katsa haka don mutane sudan samu karsashin alqawarin da aka yi musu ganin zave ya taho ba a yi hanyar ba. Iya abinda zan iya faxa kenan a nan. Za ka kashe gari ka raya daji, ka zo ka kewaye gari, ka mayar da hanya daji, kuma ka zo ka katsa ta baka yi ta ba, don haka ni a fahimta ta kawai aika-aika aka yi ba aiki ba. motyoci ba sa abi Babura ba sa bi ka ga ba ta zama hanya ba. har halin da ake ciki yanzu, amma na cewa an yi hanya. Ni ba wai ina adawa da ka bane, in an yi zan ce an yi. Misali lokacin da muna jam’iyyar adawa, na yi ANPP, na yi CPC, na yi PDP, na yi APC, kuma ni ra’ayina idan ka shigo cikin jihar Ktsina na san z aka iya sukan jam’iyyar PDP a wani abin, amma ba a aiki ba. wannan shi ne abin zan faxa
To madalla mun gode.
Ni ma na gode.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!