Amfanin Kindirmo (Nono) A Jikin Dan’adam — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KIWON LAFIYA

Amfanin Kindirmo (Nono) A Jikin Dan’adam

Published

on


Shan kindirmo na da amfani sosai ga koshin lafiya, ciki har da kyautata yanayin hanji. Shan kindirmo na taimakawa wajen hana kwayoyin cuta shiga hanji da kyautata motsin hanji, hakan za a iya hana kullewar ciki.
– Shan kindirmo na taimaka wa jikin mutum wajen samun abubuwa masu gina jiki daga madara. Kwararru sun ba da shawara cewa, kamata ya yi a kullum mutane su rika shan kindirmo.
-Shan kindirmo na taimakawa wajen samu kiwon lafiya. Bisa nazarin da aka yi an nuna cewa, shan kindirmo na kosar da mutum har ma ya hana shi kara cin wani abincin, wannan wata hanya ce ta rage nauyi. Idan an tsaya tsayin daka kan shan kindirmo a kowace rana, to za a rage nauyi cikin.
-Shan kindirmo na taimakawa wajen kara karfin gashin mutum. Kwararru a fannin kimiyya da fasaha suna ganin cewa, sinadarin Calcium na da amfani ga goshin mutane ko tsofaffi ko kuma yara. Sinadarin Bitamin D da ke cikin kindirmo na iya taimaka wa mutane wajen samun sinadarin Calcium.
-Shan kindirmo na taimakawa wajen kara karfin goshi.
– Shan kindirmo na iya rage hawan jini. Bisa nazarin da aka yi an nuna cewa, a cikin mutanen da suke shan kindirmo a ko wace rana, yawansu da ke fuskantar yiwuwar kamuwa da hawan jini ya ragu da kashi 50 cikin kashi 100, idan aka kwatanta su da wadanda ba su shan kindirmo kwata-kawata. Bugu da kari, shan kindirmo na iya kyautata yanayin hanji, da kuma kara kwayoyin da ke ba da garkuwa ga jikin mutum daga kamuwa da cututtuka.
Ga matan da ke fama da ciwon sukari, idan za su yawaita shan kindirmon da ya kai mita 200 a ko wace rana, hakan na iya taimakawa wajen hana kamuwa da kwayoyin cututtukan da ke shafar mata. To, yaya za a iya shan kindirmo yadda ya
kamata? Sanin kowa ne cewa mutane sun bambanta, wasu kan sha kindirmon da ya kai kofuna 1 zuwa biyu, mita 250 zuwa 500 a ko wace rana. Ga yara kuma ya fi kyau su sha madara kofi 1 da safe da kuma kindirmo kofi 1 da dare. Ga wadanda ke fama da cututtukan da suka shafi ciki da hanji kuma, suna iya kara yawan kindirmon da suke sha a ko wace rana don samun abubuwa masu gina jiki da kyautata yanayin ciki da hanji ta yadda za a kara kwayoyin da ke ba da garkuwa ga jikin mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma kara saurin samun warkewa daga cututtukan. A hakika dai, ana iya shan kindirmo a ko wane lokaci. Amma mutanen da suke fama da ciwon ciki ba su iya shan kindirmo a yayin da suke jin yunwa. Ban da wannan kuma, bai kamata mutanen da su ke fama da ciwon ciki a yayin da suke jin sanyi su sha kindirmon da suka fitar daga firiji ba da dadewa ba saboda sanyin da ya yi. Ya kamata a ajiye shi na tsawon rabin awa tukuna kafin a sha.

•Dimbin Amfanin Gishiri Ga Dan’adam
Kwararru a fannin kiwon lafiya sun tabbatar cewa bayan abin da muka sani na al’ada wato amfanin gishiri cikin miya, hakika sun tabbatar cewa gishiri dai yana da dimbin sirruka da amfani ga dan’Adam. Wanda ake amfani da shi na abubuwan yauda kullin a kan kira shi da wasu sunaye kamar haka:
English- Salt.
Arabic- Milh.
India- Nun.
China- Yan-Yan.
Yoruba – Iyo.
Igbo- Nnu.
Hausa- Gishiri.
Ga wasu daga cikin amfanin sa gishiri:

-Kowa ya san cewa idan kyandir ya diga a waje, tilas zai manne da wajen har sai an kankare shi da karfin tuwo, amma muddin aka ji ka kyandir din na tsawon awa biyu ko uku, to da zaran an kunna shi yana ci ko da zai diga a waje ba zai kama ba. Za a
sha mamaki domin da an dan murje shi zai fita tamkar kyandir bai taba diga wajen ba.
– Ina mata masu amfani da risho ko abin gashi irin na lantarki ko wanda ake amfani da gas? Mafi yawan lokaci idan kina girki za ki ga ruwan girkin ko man gyada da ki ka yi suya da shi ko dai wani abu da ki ka dafa a kan risho ya bata shi sosai, kafin kuma ki gama girkin ya bushe, don haka da rishonki ya fara baci sai ki barbada gishiri a wajen, da kin gama girki idan ya huce kina saka soso za ki ga ya fita. Haka ma za ki yi wa dukkanin ababen girkin ki.
– Idan kina tantaman kwai ko ya lalace ko yana da kyau, sai ki zuba gishiri karamin cokali biyu a cikin ruwa ki kada, ki zuba kwan a ciki, idan yana da kyau za ki ga kwan ya taso sama yana yawo, idan kuma ya lalace ne za ki ga ya yi kasa, sabanin abin da aka saba gani.
– Sosan wanke-wanke idan ba a tsaftace shi sai ya zama waje ne da kwayoyin cuta suke shiga a ciki don haka duk lokacin da ki ka gama wanke-wanke ki wanke sosan sosai, sai ki jika shi a cikin ruwan gishiri na awa daya ko biyu da zarar kin ga ya fara lalacewa ki yar da shi ki sayi wani.
– Idan kin sayi tsintsiya kuma kina so ta dade miki, kafin ki fara amfani da ita sai ki jika ta a cikin ruwan gishiri kafin ki fara amfani da ita.
– Idan zuma ta harbe ki, sai ki yi sauri ki zuba ruwan gishiri a wajen, yin hakan
zai rage zafin harbin zuma kuma wajen ba zai tashi ya yi ja ba.
– Amfani da ruwan gishiri mai dumi a lokacin da mutum yake fama da ciwon hakori da kuma ciwon makogaro yana kawo sauki, sai dai da kuna, idan kika daure kunar na wani lokaci ne, amma kafin jimawa za ki ga kin sami sauki.
– Ina masoya masu aikewa da junansu fulawa ko kuma masoya fulawa? Amma fulawar da nake nufi fulawar roba, na san ba kowa ne zai zauna ya goge fulawar ba idan ta yi datti ko kura, domin lungu da sakon da take da shi. Ki tsoma fulawar a cikin ruwan gishiri na dan mintuna ki girgiza, dukkan dattin da ya ke jiki zai fita.
– Idan kina da madarar ruwa kuma tana saurin lalacewa, sai ki zuba gishiri dan kadan a ciki ki jijjiga ki rufe.
– Idan jini ya bata miki kaya sai ki jika su a cikin ruwan gishiri ki wanke sannan ki saka su a cikin ruwan dumi da omo ki wanke. Haka kuma idan gumin hammata ya bata miki kaya sai ki zuba gishiri a cikin ruwan dumi ki wanke kayan.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!