Babban Bankin Nijeriya Ya Fara Sayar Da Kudin Kasar Sin — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Babban Bankin Nijeriya Ya Fara Sayar Da Kudin Kasar Sin

Published

on


A jiya Juma’a Babban Bankin Nijeriya ya fara sayar da kudin kasar Sin, Yuan a kasuwar shinku.
Fara sayar da kudin na Sin na nuna aiki da yarjejeniyar da aka cimma a tsakanin Bankin da Babban Bankin Sin kan musanyar kudaden kasashen biyu a watan Afirlun 2018.
Babban bankin ya yi bayanin cewa za a ci gaba da sayar da kudin kasar ne a karkashin yarjejeniyar da aka cimma da ta hada matakin gajeren zango da na dogon zango.
Sanarwar da mai magana da yawun Babban Bankin na CBN, Mista Isaac Okafor ya fitar a jiya Juma’a ta yi bayanin cewa sayar da kudin na Sin yana karkashin tsari ne na musamman da ya kunshi ba da canji domin sayo kayan da ake son sarrafawa a cikin gida, da na’urori da kuma abubuwan da suka shafi aikin gona.
Sanarwar ta ce CBN zai saurari gabatar da bukatar sayar da kudin na Sin daga dilolin da doka ta amince da su.
Ta kara da cewa saboda yanayin tsarin sayar da kudin, babban bankin ba zai nemi yin garambawul ga ka’idojin sayar da kudaden waje a kasuwar bankuna ba, wadda a ciki aka umurci gabatar da bukatar neman sayar da kudaden ga CBN ta hannun manyan dillalan sayar da kudaden waje.
“Har ila yau, CBN ba zai nemi yin kwaskwarima ga tanade-tanaden ka’idojin sayar da kudaden wajen da suka bayyana cewa duk wani wurin sayar da kudaden waje ga masu amfani da su kai-tsaye ba zai samu fiye da kashi daya bisa dari na yawan dukkan adadin kudin da ake da su a hannu ba lokacin da za a yi rabonsu.”
Da yake karin haske kan lokacin da za a gabatar da bukatar neman sayar da kudaden, Mista Okafor ya ce dilolin da doka ta amince da su an nemi kowa ya gabatar da bukatar masu saye a hannunsu daga karfe 9 na safe zuwa 12 na ranar Juma’ar jiya, 20 ga watan Yulin 2018, inda ya ce duk wanda bai gabatar a tsakanin lokacin ba ya rasa.
Dangane da biyan kudin sayen kudaden na Sin kuwa, ya ce ana bukatar dilolin da doka ta amince da su su cire adadin kudin Naira da ake son karbar canjinsu daga asusun masu hulda da su tare da bayyana cewa CBN kuma zai cire kudaden da aka biya daga asusun dilolin na Naira a ranar da za a raba kudaden na Sin.
Mista Okafor ya kuma ce za a bari dilolin su samu ribar kobo 50 a saman kudaden da masu hulda da su suke son sayen kudin na kasar Sin da su.
Wannan dai ba karamin ci gaba ba ne ga ‘yan kasuwan Nijeriya da ke hada-hada a tsakanin Sin da Nijeriya, kasancewar a yanzu kai-tsaye za su iya amfani da Yuan da Naira a tsakaninsu da takwarorinsu na Sin ba tare da sun yi canjin kudin zuwa Dalar Amurka ba.

Advertisement
Click to comment

labarai