Kwalejin Kangere Na Neman Naira Miliyan Dari Don Gyara Barnar Da Guguwa Ta Yi Mata — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Kwalejin Kangere Na Neman Naira Miliyan Dari Don Gyara Barnar Da Guguwa Ta Yi Mata

Published

on


Kwalejin ilimi ta Adamu Tafawa Balewa da ke Kangere ta bayyana cewar Naira miliyan dari daya take da bukata domin gyara muhallan da Guguwa ta lalata a cikin kwalejin a ranar 16 ga watan Yuni na 2018.
Shugaban kwalejin Dakta Garba Ibrahim Kirfi shi ne ya shaida hakan ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da Jami’in watsa labarai na kwalejin Bala Baban Kawu ya raba a jiya Juma’a.
Kirfi ya bayyana cewar hakan ya faru ne a sakamakon ruwa da iska mai karfin gaske da aka samu a kwanakin baya.
Kirfi ya kara da cewa, Kwamfuwutoci, littafai, kayyakin koyarwa, dakunan kwana da dakunan karatu, gidajen kwanan malamai da na daliban da suke wannan kwalejin duk wasu sun lalace a sakamakon wannan ibtila’in.
Ya bayyana cewar a bangaren littafan da suka lalace kadai, kwalejin na neman Naira miliyan 50 domin maye gurbin wadanda suka lalace, “A cikin dakin bincike na karatu, littafan da suka lalace, sai an samar da kusan miliyan 50 kafin mu iya maye gurbinsu,” In ji Kirfi.
Ya kara da cewa, daga cikin littafan da suka hada har da bayanan daliban da na karatunsu da dama ruwan ya lalata, inda ya bayyana cewar sai an tashi tsaye kafin a samu nasarar daidaito da komai a cikin kwalejin.

Advertisement
Click to comment

labarai