Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Kori ‘Yan Sanda Hudu Saboda Damfarar Fasto Naira Miliyan 7

Published

on

An kori ‘yan sanda guda hudu na SARS a jihar Legas saboda samun su da kwarewa wajen rashin ladabi, cin hanci da rashawa da kuma rashin gudanar da aiki yadda ya kamata. ‘Yan sandan da aka kora su ne Adeoye Adekunle da Adeniran Adebowale da Agbi Lucky da kuma Odighe Hehosa.

Kuto ta tuhume su da laifin fashi da makami, garkuwa da mutane, ba da tsoro a kan wani Fasto mai suna Mista Chukwudi Odionye.

Mai Magana da yawun ‘yan sanda na yankin zone 2 CSP Dolapo Badmus a nasa bayanin yana cewa ya samu karar da Odionye ya kai a kan ‘yan sanda guda hudu a ranar 2 ga watan Mayu na shekaran 2018.

A karar da Odionye ya ce ranar 4 ga watan  Yuni na shekara ta 2017, yana cikin gidansa a yankin Alagbado na Jihar Legas sai wadan nan ‘yan sanda guda hudu suka kutsa ciki, suka kama shi a kan wai suna zarginsa da yin mu’ujiza ta karya.

Ya ce “Bayan sun kamani, sun ajiyeni a wani Otal dake Agege inda za su kai ni in dai ban basu hadin kai ba. Ya kara da cewa washe garin ranar 5 ga watan Yuni na shekaran 2017, sai suka tafi da ni banki wai in tura naira miliyan 7 a asusun ajiya na wani dan sanda”.

Da yake sauraran karar, mataimakin shugaban ‘yan sanda na yankin zone 2 AIG Adamu Ibrahim ya ba da umurnin a je abincika. A binciken da aka yi, ya bayyana cewa ‘yan sandan guda hudu na SARS sun kama Odionye domin bukatar kansu ce kawai.

Mataimakin Shugaban ‘yan sandar ya dakatar da wadannan ‘yan sandan ne bayan ya same su da laifuffuka kamar su rashin ladabi, ayyukan cin hanci da kuma rashin bin dokar aiki. ‘Yan sandan an garzaya da su kotun ake sauraran maiyan laifuka kamar su fashi da makami, sata da kuma tada zaune tsaye.

Badmus ya ce mataimakin Shugaban ‘yan sanda ya ce, hukumar ‘yan sanda ba za ta lamunta ba ga  duk wani rashin ladabin da zai gurgunta aikin ‘yan sanda, duk wani dan sanda aka samu da laifi ba za a taba kare shi ba.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: