Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Saurayi Ya Rataye Kansa Saboda Matsalolin rayuwa

Published

on

Tolulope Kolawole ya rataye kansa, saurayin da ne ga Misis Olufunke Kolawole wadda babba sakatariya ce a ofishin gwamnar jihar Osun.

An bayyana cewa saurayin ya rataye kansa ne saboda matsalolin rayuwa da yake fuskanta.

Mazauna rukunin gidaje dake Halleluya a garin Osogbo inda yake zaune sun shaida wa manema labarai ranar Asabar cewa, a ranar Alhamis ne dan shekara 32 da haihuwa mai suna Tolulope ya rataye kansa.

Mahaifiyarsa mai suna Olufunke Kolawole an sace ta a hanyarta na zuwa Abuja domin yin wani muhimmin aiki sannan daga bisani aka kashe ta a shekaran da ta gabata.

Dan da ta bari mai suna Tolulope ya dade yana korafi a kan koma bayan da yake samu a gonar da yake kula da ita.

Wani mazaunin yankin mai suna Remi Taiwo ya bayyanawa manema labarai cewa shi abokinsa ne a garin Ibadan na Jihar Oyo, ya bayyana masa cewa yana fuskantar matsaloli kuma har matarsa ta fara kokawa a kan lamarin.

Ya kara da cewa “akwai wani abokinsa wanda ban iya tuna sunan shi ya ce masa zai taimaka masa da kudi, na gargade shi a kan kar ya sake ya bi hanyar da baidace ba domin kawo karshin matsalolnsa”.

Majiyar ‘yan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin ta wayar tarho, sun ce, sun samu labarin lamarin ne ta ofishinsu dake dada sannan daga bisani suka mai da lamarin zuwa ofishinsu na garin Osogbo dake Jihar Osun.

Wata majiya ta bayyana cewa matashin ya so ya samu wani kaso daga cikin kudin mahaifiyansa dake kasuwanci da su. Ya ci gaba da cewa kullum yana korafi a kan abokinsa na garin Ibadan cikin Jihar Oyo wanda ya ce zai taimaka masa da kudade, lokacin da ya ga ba zai samu ba sai ya rataye kansa. Ya saka igiya a wuyansa sai ya hau kan kujera amma kafin wani ya zo sai ya shure kujeran. Matumin da ya gansa sai ya yi sauri ya kira matanan gidan, lokacin da mutane suka zo sun taradda ya mutu.

Majiyar ‘yan sanda sun ce duka matanin dake cikin gidan su marigayin sun garzaya zuwa ofishin ‘yan sanda don sanar musu da lamarin.

Mai magana da yawun ‘yan sanda Miss Folasade Odoro ta ce har zuwa yanzu ba ta samu wani sakon waya ba dangane da lamarin.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: