Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Jami’an Sojoji Sun Hana Wani Bature Da Dan Sanda Karya Dokokin Hanya A Legas

Published

on

Cunkosan ababan hawa ya cunkushe babban yanyar Legas zuwa Abeokuta a babban garin kasuwancin Nijeriya wato Legas.

Tracy Sylbester ta ruwaito cewa jami’an sojojin sun hana wani bature da kunma dan sanda karya dokokin hanya.

A shinta ta sada zumunta na Twitter ta bayyana cewa “abun ya fare ne a karamar hukumar Egbeda ta jihar Legas, lokacin da nake cikin inda matoci ke tsayawa a Egbeda ta jihar Legas a ranar Lahadi, akwai mahaukacin cinkosan ababan hawa a daya hannun na hanyar, dayan  hannun kuma babu cinkoso. Suna cikin tafiya sai dan sanda ya sauko daga mota don ya tsaida motoci domin juya zuwa daya bangaran hannun da ba cinkoso”.

Bai wuce sakan 10 da koma wansu sai mutanan unguwar suka rufe hanya dawata mota  karar Ledus suna zanga-zanga, sai wannan dan sandar ya kara saukowa da fishi ya ce ma wannan mai motan ya matsa daya bangaran. Ashe a cikin motan nan akwai jammi’an soja 3 sai suka ce mai yake faruwa ne? wadannan sojoji sai suka je wajen motar ‘yan sandar, lokacin ne aka gane cewa ashe bature ne a cikin matar. Sai yana ta sojojin nan hakuri ,su kuma suka ki hakura tare da ce mishi idan za su bi dokar hanya a kasarsu to mai zai hana shima ya bi dokar kasarsu.

Sojojin daga baya sun bude hanya tare da bai wa mutane hakuri sannan shi kuma baturan suka ce masa ya koma can baya wajen cinkosan.

Dukkan mutanan dake wajen sun yaba wa sojojin, na so dauka a waya amma ziciyana bai kowa min hakan ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: