Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Lauyoyi A Jihar Imo Sun Tsayar Da Aiyyukan Kotu Saboda Musgunawa Da ‘Yan Sanda Keyi Musu

Published

on

A ranar Litinin da ta gabata kungiyar Lauyoyin reshan jihar Imo sun tsayar da aiyyukan Kotu saboda za su gudanar da zanga-zanga na kwana uku domin zargin ‘yan sanda da musgunawa ‘ya’yanta.

Lokacin zanga-zangar dai Louyoyin suna daga kwalaye wanda aka rubuta cewa “ shugaban ‘yan sanda ya hukunta Kwamishinar jihar Imo”  wasu kuma sun rubuta cewa “ hukumar ‘yan sanda ta salami mataimakin ‘yan sandar jihar wanda ya jagoranci farmakin Louyoyin”.

Lauyoyin sun  bukaci Kotu da ta sa hukumar ‘yan sanda su bincike wanda suke da hannu a cikin wannan al’amarin.

Shugaban kungiyar Mista Damian Nosike ya gaya ma kafar yada labarai na Nijeriya

Baya zanga-zangar cewa Lauyoyin sun kauracewa zaman Kutu na tsawan kwana uku. Ya kara da cewa bayan wannan kauracewa, kungiyar za su dauki mataki a kan ‘yan sanda domin su dunga aiki yadda ya kamata.

Nosike ya yi kira da a hukunta Kwamishinan ‘yan sandar jihar Imo Mista Dasuki Galadanchi da kuma shugaban sashin ‘yan sanda Ngor-Okpala saboda jajorantar kai wa Lauyoyi hari. Ya kara da cewa bai kamata a ce ‘yan sanda sun kai wa Louyoyi hari, ya ce reshan kungiyar zai bi diddigin lamarin har zuwa karshe.

Alkalin Kotun Magistrates na karamar hukumar Ngor-Okpala yana zargin Lauyoyi guda biyu Emma Eke da kuma Chukwuemeka Anyanwu  da hadin bakinsu ne mutane uku wanda ake zargi da laifin fashi da makami  suka gudu.

Saboda haka shi ya saka DPO na Ngor-Okpala SP I.E Moses ya mamaye Kotu domin su kama Lauyoyin nan guda biyu.

Lauyoyin wadanda ake zargi a gaban Kotu ranar Jumma’a domin ci gaba da sauraran karan.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: