Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Wata Budurwar Data Yi Shirin Karya Na Garkuwa Da Kanta Ta Shiga Hannun ‘Yan Sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cefke wata budurwa ‘yar shekara 19 da haihuwa mai suna Dorcas Adilewa saboda laifin shirin karya na garkuwa da ita domin cutar da mahaifinta.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito cewa ita wannan budurwa ta hada kai ne da wata kawar ta mai suna Ifeoluwa Ogunbanjo wanda ta samar mata da wajen zama da kuma wayan  salula domin ta kira iyayanta.

Kwamishinan jihar Legas Imohimi Edgal ya ce sun cefke yarinyan ne ranar 13 ga watan Yuli sakamakon rahotan da mahaifanta ya kai ofishin ‘yan sandar dake Ketu.

“ A ranar 7 ga watan Yuli da misalin karfe biyar na yamma, Adilewa Taiwo ya amsa kiran wayan salula da wannan nambar 09057432362 a Ofishin ‘yan sandar Ketu  mai namba 3 dake layin Kosumi a garin Bello-Ketu.

“Ya ce yarinyansa mai suna Dorcas Adile an yi garkuwa da ita idan baya so a kasha ta to ya biya kudin fansa naira 600,000 kafin a sake ta.

“ Binciken gaggawa da aka gudanar na wayan salula ya nuna cewa wanda ake zargi suna cikin yankin Ijebu-Igbo na jihar Ogun.

“ Rundunar ‘yan sanda masu binciken laifuffukan garkuwa da mutane sun gudanar da bincike a duk yankin Ijebu-Igbo ranar 12 ga watan Yuli domin su zakulo wadanda ake zargi”.

Kwamishina ya ce lokacin da ake bincike a Ijebu-Igbo inda ake tunanin masu girkuwan suna ciki, sai binciken ya nuna cewa su bar Ijebu-Igbo su koma Ikotun ta jihar Legas domin su ceto wanda aka sace.

“Lokacin da mai garkuwan ya tabbatar da ‘yan sanda sun kusan kama su, sai ya kira waya yana cewa ai an sake ta, bayan an saka masa naira 8,000 a asusun ajiya na bankin UBA mai namba kamar haka 2087804991.”

Mista Imohimi ya ce lokacin da ake tuhumi Adilewa a kan sakin da aka yi mata, ta shaida cewa kamata da aka yi duk shirin karya ne da suka hada ita da abokiyanta Ogunbanjo.

“ Ta samar mata da wajen zama mai namba 174 dake layin Adeboye cikin Okesopin a jarin Ijebu-Igbo na jihar Ogun tare da kiran wayan salula dok samun kudin fansa.

“Idan aka gama gudanar da bincike za a tura su Kotu” inji Kwamishina.

A daya bangaran kuma, ‘yan sandar jihar Legas sun cefke wani mutum mai suna Jacob Dare saboda yunkurin garkuwa da mutane.

Imohimi ya ce sun samu rahotan wannan al’amarin ne a ofishinsu na sashe dake Ayobo ta jihar Legas a ranar 17 ga watan Yuli. Ya kara da cewa shi wanda ake zargi ya yi kokarin sace wata yayinya a Coci mai suna Christ Anointed na Ayobo dake jihar Legas.

Kwamishina ya ce  wanda ake zargi ba mabiyan wannan cocin ba ne, ya yi kokarin yin garkuwa da yarinyan ne ta yanyar jan hankalin ta da kyautar naira hamsin. Ya kara da cewa wanda ake zargi ya yi kokarin gudu  lokacin da abun ya faru amma mutanan cocin sun yi nasarar kama shi.

Imohimi ya ce shi wanda ake zargi ya musanta al’amarin tare da cewa shi fa mahaukaci ne amma daga baya ya ce shi mai hankali ne kuma ya zo coci ne domin ya yi ibada.

“Ya kare kansa a kan lamarin kokarin yima karamar yarinya wayo da naira 50, ya ce shi kawai yana tambayan yarinyan tare da mamanta hanya ne kawai”.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: