Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Haramta Wa ‘Yan Sanda Sintiri A Cikin Farin Kaya A Legas

Published

on

Kwamishinar ‘yan sandar jihar Legas Edgal Imohimi ya haramta wa ‘yan sanda masu sintiri a cikin farin kaya lokacin da suke a bakin aiki.
A cikin bayanin da aka samo daga zafin sada zumunta na Facebook, ‘yan sanda sun ce dalilin daukan wannan mataki shi ne don ya tabbatar da kwarewarsu. Bayanin da mai magana da yawun ‘yan sanda CSP Chike Oti ya rattabawa hannu tare da karanta wani bagaran “ domin a tabbatar da kwarewar ‘yan sanda a fadin jihar Legas baki daya, Kwamishinar jihar Legas CP Edgal Imohimi ya hana ‘yan sanda sintiri a cikin farin kaya tare da hawa motocin bas wanda ake haya da su dake kira da suna Danfo dama sauran motoci haya a duk fadin jihar. Motocin da bana aiki ba, za a yi amfani da su ne kawai wajen wani aiki na musamman ko wani taro na daban”.
A cikin bayanin, hukumar ‘yan sanda ta tona asirin masu amfani da kayan ‘yan sandar da ake kira SARS suna fashi da makami da su. Domin samun kariya daga cikin aiyukan mutane, Kwamishinan ya yi bayanin irin tsarin kayan ’yan sandar SARS. Ya ce suna da kaya na musamman wanda suke sawa mai dauke da tambarin hukumar ‘yan sanda.
Kwamishinan ya yi wa mutane bayani cewa duk wani dan sandar da suke korafi, to su gaggauta kai karanshi wajen hukumar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: