Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Zartaswa Da Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Laifin Kashe Lauya

Published

on

A ranar Alhamis ne babban Kotun jihar Sakkwato ta yanke ma wani mutum mai suna Atiku Galadima dan shekara 37 da haihuwa hukuncin kisa ta hanyan rayewa bisa laifin kasha Lauya mai suna Sirajo Abubakar. Alkali Bello Duwale ya ce an samu shaidu wanda suka tabbatar da cewa lalle da gangan ya kasha shi. Alkalin ya yi watsi da duk wata shaida da take nuna cewa bada gangan ya kasha shi ba kamar yadda sashin 220 na penal code ta tanadar.
Shaidu sun nuna cewa ya taba shakure Abubakar a ranar 3 ga watan Yuni na shekarar 2012 sai ya gudu Kaduna kafin a cafke shin shekarar 2016. Alkalin ya kuma same shi da kai wa wani shugaban makaranta hari mai suna Yakubu Sani, wadan sune kadan daga cikin hujjojin da suka tabbatar cewa dagangan ya kasha shi. Alkalin ya kara da cewa wannan hujjojin su suka saka Galadima yin hijira na tsawan shekaru hudu. Alkali Dawale ya ce “saboda haka na kama shi da laifin.
“yadda sashin 221 B) tsarin dokar Penal Code ta tanadar, wanda aka samu da laifi irin wannan sai a kasha shi ta hanyar ratayewa,” inji shi.
Duwale ya bayyana cewa Galadima yana da damar daukaka kara kafin wata uku.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: