Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sandan Jihar Zamfara Sun Cafke Kasurgumin Dan Ta’adda

Published

on

Rundunar ‘yan sandar jihar Zamfara sun samu nasarar cafke kasugumin dan ta’adda a wani samame da suka kai a garin Chali da Gobirawa ta karamar hukumar Maru cikin jihar Zamfara. Shi dai wanda aka kama da ne ga yar kanwan Buharin-Daji.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Zamfara Mista Kenneth Ebrimson ya ce lokacin da aka kama dan ta’addan sun gabartar da shi a gaban ‘yan jarida ranar Talata a garin Gusau. Ebrimson ya kara da cewa, gungun ‘yan ta’addan sun yi yunkurin kai hari a wasu kauyuka guda biyu ranar 23 ga watan Yuli, wannan shi ya fusata ’yan sanda suka yi dabarun aiki don su kama su.
“Lokacin da muka samu masaniyar sai muka hada jami’anmu masu yaki da ta’addanci da kuma ‘yan sandar mobayil domin su dakile harin.
“Sun tsunduma cikin ‘yan ta’addan da bindigogin yaki, yayin da suka samu nasarar kama daya daga cikin su sauran kuma suka gudu.
“ Dan ta’addan mai suna Zakoa Buhari shi dai dan kauwa ne ga Buharin-Daji wanda aka kasha a watan Afrilu na wannan shekaran.
“An same shi da bindiga karan AK-47 tare da harshashinta guda biyu sai kuma harshashi guda 77 masu cikin nisan mita 7.62,” inji shi.
A cewar Kwamishanar ‘yan sanda, dan ta’addan da aka kama yanzu haka yana wajen jami’an ‘yan sanda yana taimaka musu da bayanai a kan sauran ’yan ta’addan.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: