Connect with us

MANYAN LABARAI

Kashe-Kashe A Zamfara: Sojoji Sun Yi Babban Kamu

Published

on

…Sun Ceto ‘Yansanda 5 Da Aka Sace
Rundunar kai daukin gaggauwa ta 207 ta dakarun sojojin saman Nijeriya sun samu nasarar damke ‘yan bingida 16 da ake zargi da aika-aika a Jihar Zamfara.
Dakarun sojin sun cafke ‘yan bindigan ne sa’ilin da suke aikin tsaro da suka yi wa lakabin ‘ofirashan sharar daji’ da ke gudana karkashin shalkwatar tsaro ta Nijeriya.
Kwamanda mai barin gado na rundunar, Guruf Kyaftin Caleb Olayera ya sanar da haka lokacin da yake tarbar Babban Hafsan Sojojin Sama, Iya Mashal Sadikue Abubakar da ke rangadin rukunonin rundunar da ke aiki a Gusau.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojojin saman Nijeriya, Iya Mashal Olatokunbo Adesanya ya rattaba wa hannu aka raba wa ‘yan jarida jiya Alhamis, ta bayyana cewa babban hafsan rundunar ya umurci kara yawan jiragen saman yaki domin tallafa wa aikin tsaron da ake gudanarwa a jihar ta Zamfara domin kara wa dakarun da ke yaki da miyagu kaimi.
A cewar Gurf Kyaftin Olalyera, baya ga dakarun sojin saman da ke gumurzu a kasa, jirgin saman yakin rundunar mai lamba 207 KRG, na aiki ba dare-ba-rana wajen tattara bayanan sirri tare da rufa-baya da karfafa dakarun da ke aiki a rundunar ta ofirashan sharer daji.
Ya cigaba da bayyana cewa a cikin ayyukan da suke yi, rundunarsu ta 207 ta yi wani babban kamu inda ta cafke wani kasurgumin dilan miyagun kwayoyi wanda ta hannanta wa Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa domin hukunta shi. Bugu da kari, rundunar ta kuma kwato bindigogi uku da albarusai masu yawa daga miyagun da aka cafke da ake zargi da aika-aika a Zamfara.
Har ila yau, ya ce dakarunsu sun ceto mutum uku ‘yan kauyen Boko da aka ji wa raunuka tare da ‘yansanda guda biyar da aka yi garkuwa da su, da kuma ‘yanto wasu mutum uku da aka sace don karbar kudin fansa.
Kwamandan rundunar mai barin gado, ya kuma yi wa Babban Hafsan Sojojin Saman bayanin kalubalen da dakarunsu ke fuskanta wanda ya ce matukar an magance su, za a kara cin nasara a aikin tsaron da suke kan gudanarwa.
A nashi bangaren, Babban Hafsan Dakarun Sojin Saman, Iya Mashal Abubakar ya yaba wa rundunar ta 207 saboda jaruntakar da suka nuna zuwa yanzu wajen tabbatar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.
Wakazalika, ya jinjina wa dabarun da dakarun ke aiki da su idan suka fuskanci hatsarin abokan gaba, kana ya tunatar da su cewa a matsayinsu na dakarun sojin da suka samu horo, suna da alhakin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya nagari.
Nasarar da dakarun sojojin saman suka samu wajen wannan babban kamun da suka yi, ta sanya ajiyar zuci ga ba al’ummar Zamfara ba kawai har ma da sauran ‘Yan Nijeriya da hankalinsu ya ki kwanciya saboda kashe-kashen da ake yi a Zamfara wanda ko ranar Laraba da La’asar sai da wasu miyagu suka kashe akalla mutum ashirin a wani kauyen da ke Zurmin Jihar Zamfara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!