‘Wasu Daga Cikin Sanatocin Da Suka Bar APC Na Shirin Dawowa’ Umar A Hunkuy — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

‘Wasu Daga Cikin Sanatocin Da Suka Bar APC Na Shirin Dawowa’ Umar A Hunkuy

Published

on


Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan, ya yi ikirari a ranar Laraba cewa, wasu daga cikin sanatocin da suka fice daga Jam’iyyar ta APC sun nuna aniyarsu ta sake dawowa cikin Jam’iyyar.
Lawan ya yi wannan ikirarin ne cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai na fadar gwamnati jim kadan da ya jagoranci Sanatoci 43 na jam’iyyar ta APC wajen wani taron sirri tare da Shugaba Buhari, a fadar ta Shugaban Kasa.
Ya kuma yi zargin cewa, wasu ma Sanatocin Jam’iyyar PDP sun nu na aniyarsu ta shigowa cikin Jam’iyyar ta APC.
Ya ce, “Bari na gaya maku, ko a jiya awanni 24 da fadin sun canza shekan, mun tattauna da wasun su, sun kuma nu na aniyar su ta sake dawowa.
“Don haka muna yin duk abin da muke iyawa tare da shugabannin Jam’iyyarmu, domin ganin mun shawo kan ‘yan’uwan namu da suka fice su dawo a kwanan nan.
Lawan ya ce, abin da ya faru a zauren Majalisar, musamman ma Majalisar Dattawa, a ranar Talata, kamata ya yi ya zama wani sabani ne na iyalai, amma sai aka yi masa hukuncin da bai kamata ba.
“Amma yanzun duk mun yanke shawarar goyon bayan Shugaban kasarmu da kuma wannan gwamnatin domin mu cika dukkan alkawurran da muka dauka a lokacin yakin neman zabe.
Lawan ya ce, ‘yan Majalisar sun shaida wa Buhari hakikanin abin da ya faru a zauren majalisar, sun kuma tabbatar masa da har yanzun dai Jam’iyyar APC ne ke da rinjaye a cikin Majalisar, duk da ficewar da wasu suka yi.
Wani Sanata daga Jihar Kaduna, Shehu Sani, cewa ya yi, shi ba shi da sauran wani korafi, domin duk matsalar da yake da ita da Jam’iyyar an warware ta bakidayanta.
Ya ce, ai babu wata matsala a kan tayar da kayar baya, ya kara da cewa, ai ita kanta Jam’iyyar ta APC, alami ce ta tayar da kayar baya ai.
Shehu Sani, ya bayyana tabbacin da yake da shi na cewa, duk wasu rigingimun cikin jam’iyyar nan ba da jimawa ba za a warware su.
Ya ce, “Ina zaune ne a nan a matsayin dan Jam’iyyar APC a wannan majalisar ta Dattawa. Zaman da nake a nan ba yana nufin an gama warware matsalolin da nake fuskanta ne ba kacokam, amma dai ina da tabbacin a yanzun muna da shugaban da yake yin duk abin da yake iyawa na ganin ya warware dukkanin sabanin da har ya kai ga tayar da kayar bayan.
“Ina da tabbacin abin da muka tattauna a nan yana bayar da tabbaci ne na kwantar da duk wata kura da ta tashi, wacce har ta kai ga matsayin da muke cikinsa a yau din nan.
‘Ina da tabbacin Shugaban Jam’iyyarmu zai iya warware dukkanin matsalolin.”
Shugaban Jam’iyyar, Adams Oshiomhole, cewa ya yi, abin farin ciki ne da na ji daga bakin shugaban masu rinjaye cewa, har yanzun dai mune muke da rinjaye a cikin Majalisar.
Tsohon gwamnan na Jihar Edo, ya yi zargin cewa da yawa daga cikin wadanda suka bar Jam’iyyar duk an rude su ne.
Ya bayyana tabbacin da yake da shi na cewa, gaskiya za ta bayyana, ya kuma san duk za su dawo ne.
Ya ce, “Ai komai ya yi kyau. Muna da Sanatoci 53 daga cikin 107. A gaskiya hakan ya yi mana daidai. A nan da makwanni daya ko biyu, muna sa ran sake kama kujerun mu biyu na rashe-rashen da aka yi mana.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!