Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Likita Da Nas Sun Shiga Hannu Sakamakon Mutuwar Wanda Suka Zubar Wa Da Ciki

Published

on

Rundunar ‘yan sandar jihar Ogun sun cafke Dakta Olawale Raji da kuma Nas Fumilayo Olusegun sakamakon mutuwar wanda suka zubar wa da ciki mai suna Aminat Atisola.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama wanda ake zargi ne tun ranar Alhamis 26 ga watan Yuli na shekara 2018.
Mai magana da yawun ‘yan sandar jihar Abimbola Oyeyemi ya ce an kama wadanda ake zargi ne sakamakon kai kara da dan uwar wanda aka kasha mai suna Bose Kazeem ya yi wanda yake zaune a Atan na Ota.
Ya ce Aminat ta samu juna biyu tun wata biyu da suka wuce kuma kalubalantar wanda ake zargi da yi mata aikin jire cikin a wani asibitin kudi.
Oyeyemi ya ce wanda ake zargi sun yi aikin jire cikin ne ba bisa ka’ida ba a jidan su marigayiyan. Ya bayyana cewa matsalar ta fara faruwa ne lokacin da Aminat ta galabaita bayan an gama aikin jire cikin sannan ta mutu yayin da aka dauke ta zuwa babban Asibitin Abeokuta. Oyeyemi kara da cewa lokacin da shugaban ‘yan sandar sashin Onipanu ta garin Ota mai suna Sangobiyi Johnson ya samu labarin al’amarin, sai ya hada tawagarsa domin su kamo wadannan mutanan guda biyun da ake zargi. Ya ce gawar Aminat yana ajiye a babban Asibitin Ota domin a gwada gawar.
A halin yanzu, kwamishinar ‘yan sandar jihar Ahmed Iliyasu ya bada da a canza wa wadanda ake zargi wuri, inda ya bada umurnin a kai su jan sashin biciken manyan laifuffuka na Abeokuta domin gudanar da kyakykyawar bincike. Ya gargadi mutane cewa “duk wanda aka kama da zabar da cikin da ba bisa ka’ida ba, to muna da hukunci mai tsanani wanda doka ta bayyana.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: