Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Sojoji Sun Cafke ‘Yan Ta’adda 20 A Jihar Nasarawa

Published

on

Rundunar sojojin Nijeriya sun cafke ‘yan fashi da makami a babban hanyar zuwa Abuja dake cikin garin Keffi ta jihar Nasarawa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun zo wucewa ne cikin motar bas kiran Nissan wajen shingin binciken sojoji. An same su da bindigogi guda 17.
A cewar Sojojin, ‘yan fashin sun ce su mafarauta ne daga jihar Adamawa kuma suna kan hanyar su ne ta zuwa Abuja domin halattar bikin mafarauta wanda kungiyarsu ta shirya a garin Abuja ranar Asabar. An samu harsashe guda 135, bindigogin gargajiya guda 2, wuka guda 1, adduna guda 3 sai kuma kwari dab aka guda 1 tare da mashi 38.
Mai magana da yawun Sojojin Birgediya Janarar Tedas Chukwu ya tabbatar da kama ‘yan ta’addan ranar Asabar, ya kuma ce suna gudanar da bincike a kan lamarin, idan sun gama sai su mika su Kotu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: