Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ango Tare Da Wasu 13 Sun Mutu A Hanyar Zuwa Shagalin Aurensa

Published

on

‘Yan sanda sun ce, mutane 14 sun rasa rayukansu ciki har da ango sakamakon hadarin mota da ya auku a Bietnam, a kan hanyarsu ta zuwa shagalin aure a ranar Litinin. Hadarin mota shi yake jawo mafi ya wancin mutuwan da ake yi a Bietnam domin mutane ba sa bin dokokin hanya yadda ya kamata ga kuma rashin kyawan hanya.
Matanan da hadarin ya rutsa da sun na ranar Litinin a garin Kuang Nam dukan su ‘yan’uwan ango ne, lokacin da suke hanyarsu ta zuwa gidan amarya, injib wani dan sanda.
Da misalin karfe 2:30 na safiya lokacin da matarsu mai dauke da mutane 16 ta yi karo da wata babbar mota, nan take mutum 13 suka mutu, dayan kuma ya mutu ne lokacin da aka garzaya da shi Asibiti.
“An mai da dukkan gawawwakin gidajensu domin a binne su, yayin da aka garzaya da wanda suka ji rauni asibiti domin shan magani.” Wani dan sanda wanda abun ya faru a gaban idonsa ya bayyana cewa bai samu damar ya yi ma manema labara bayani ba saboda ba a shi damar ba. Hukumomi sun bayyana cewa suna binciken lamarin domin samun bayani a kan binda ya janyo musabbabin hadarin.
Mutane 8,200 suka mutu a shekaran da ta gabata a Bietnam sakamakon hadarin mota yayin da 8,600 suka mutu kafin shakaran da ta gabata, yawancin wannan mutane sun mutu ne a kan babura.
Yawancin hanyoyin biranan Bietnam kamar su Hanoi da kuma Ho Chi Minh cushe suke makil da zarga-zargar babura da motoci.
Don yaka ne, kungiyar direbobi ta bukaci a kara fadada hanyoyi ta yadda za su samu damar kai kayayyaki cikin kasar ta Bietnam baki daya harma da wadansu makwantar kasan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: