Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan sanda Sun Cafke Wani Dauke Da Kwayar Dala Miliyan 1.3

Published

on

Dilolin miyagun kwayoyi sun shiga hannu bayan da suka boye tabar heroin wanda darajanta ya kai fam miliyan 1 a cikin abubuwan kasha wuta.
Wannan mutane guda uku an yanke musu hukuncin zama a gidan kaso na tsawan shekara 16 da rabi bayan da aka same su da laifin safarar miyagun kwayoyi.
Jagoran mai suna Conrad Jones an kama shi da abubuwan da ke kasha wuta cike da tabar heroin wanda nauyinsa ya kai 10 dajarsa kuma ta kai na fam miliyan 1 a cikin mota kirar Ledus.
An tsaida shi a ofishi mai lamba A46 kusa da Warwicshire bayan an gama ganawa da Yassin Halgane a layin Spring ranar 7 ga watan Janairu. Sashin kula da manyan laifuka na Rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar cafke Jones bayan da suka samu bayanan sarri a cikin wayarsa na salula. Rundunar ta samu bayanan sirri wanda ake nada a cikin wayar Jones wanda yake nuna suna sarrafa miyagun kwayoyin tare da Halgane da kuma Stuart Barratt.
Jami’an sun ce, mutanan sun yi kokarin boye muyagun kwayoyin sannan daga baya da aka farmaki gidan Barratt a layin Bell Green dake Cobentry sai aka samu hodar Iblis mai nauyin 3 wanda darajarta da kai fam 300,000 a ranar 20 ga watan Oktoba.
Jones dan shekara 52 wanda yake zaune a Cobentry, an shaida yana safarar tabar heroin da kuma hodar Iblis dun daga watan Oktoba na shekaran 2017 har zuwa watan Fabrairu na wannan shekaran. A ranar Laraba ne wata Kotu dake Birmingham ta yanke masa hukuncin daurin shekara16 da rabi a gidan kaso.
Halgane dan shekara 28 da haihuwa wanda yake zaune a Southwark, an same shi da laifin safarar tabar heroin kuma an yanke masa hukuncin daurin shekara 9 a gidan kaso.
Barratt dan shekara 54 da haihuwa wanda yake zaune a Cobentry, an daure shi na tsawon shekara 8 a gidan kaso domin samun shi da laifin safarar hodar Iblis da aka yi.
Mai sari’a Mark Palser wanda yake zaune a ROCU ya ce, “ wadannan mutane sun aikata babban laifi wajen safarar muyagon kwayoyi amma saboda jajarcewa na jami’anmu ya sa aka samu nasarar cefke su.
“babu wanin boye-boye kowa ya san safarar miyagun kwayoyi na iya zulluntar al’ammarmu amma mu kuma zamu yi kokin yakan abin.
“ ya kamata wannan hukuncin ya zama izna ga duk mai aikata wannan laifin domin ba zamu laminta ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: