Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Cafke ‘Yan Fashi Biyar Sanye Da Kayan Sojoji

Published

on

Rondunar sojojin Nijeriya ta samu nasarar cafke ‘yan fashi a yankin Felele kusa da babban titin Lokoja-Okene ta Jahar Kogi. Sojojin sun ce, sun kama ‘yan fashin ne sanye da kayan sojoji suna fashi a kan babban yanya. Sojojin sun bayyana sunayansu kamar haka Sabiour Denis dan shekara 39, Isaac Donald dan  shekara 35, Joseph Isah dan shekara 35, Janet Isah da kuma Oyinoye Ochefije.

Na karshan guda biyu duka mata ne wanda sojojin ba su bayyana adadin shekarunsu ba.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa, dan fashi guda daya ya rasa ransa, mai suna Atsen sakamakon musayar wuta da aka yi tsakaninsu da sojoji.

Mai magana da yawun sojojin Bri. Gen. Tedas Chukwu ya tabbatar da Kaman, inda ya ce abubuwan da aka samu a hannunsu sun hada da bindiga kiran AK-47 cike da harsashi guda 28 da kuma kayan sojoji guda 4. Ya kara da cewa “ rundunarmu tasha samun sakonni cewa, ‘yan fashi suna saka kayan sojoji suna fashi a Felele kan babban titin Lokoja-Okene.”

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: