Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Magidanci Ya Rataye Kansa A Legas

Published

on

Mazauna unguwar Morounfolu cikin karamar hukumar Ogba dake jihar Legas sun kadu matuka bisa mutuwar mai gyaran jenareta Olatunji Opadiran wanda ya rataye kansa. Majiyarmu ta bayyana mana cewa Opadiran ya rataye kansa ne a kan fankar sama dake cikin dakinsa ranar Litinin. Mijiyar ta ce, Opadiran ya fita tun da sassafe tare da abokanansa bai dawo ba yar sai karfe 6:00 na yamma lokacin da ya aikata lamarin.

Wani mazaunin unguwar da yake bayani a kan lamarin ya gayama wakilinmu cewa, Opadiran bai nuna wani alama zai rataye kansa ba. Ya kara da cewa, Opadiran ya gaya wa abokansa kawai shi dai zai ce ya kwanta a gida. Ya ce “Ya dai fita tun da sassafe tare da abokansa guda uku, ya dawo cikin fushi sai abokinsa ya ba shi abinci.

“Bayan ya ci abinci sai abokinsa ya tafi gidansu, bayan wani lokaci sai ya dawo yana neman shi domin yana tunanin ya kwanta bacce kamar yadda ya saba idan ya gaji yake yi.

“Bayan ya ta buga kafa tare da kiran sunansa amma ba a amsa ba, sai ya belle kafan sai ya ganshi rataye saman igiya ya mutu. Ya kara labarta cewa, mutuwar Opadiran ta ba wa mazauna unguwar mamaki. Ya ce, baban marigayin ya fita tun da safe amma koda ya dawo ba a bar shi ya ga gawar ba.

Mun samu labarin cewa yan’uwansa za su gudanar da shagulgula kafin a yi masa jana’iza” inji shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar CSP Chike Oti ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa a yanzu haka an ajiye gawar a babban asibitin Ifeko. Ya kara da cewa “Mun samu labarin aukuwar lamarin da misalin karfe 6:00 na yamma a wayar tarho cewa, Olatunji Opadiran ya rataye kansa kuma muna gudanar da bincike kan lamarin.”

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: