Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Yan Sanda Sun Cafke Magidancin Da Ya Yi Wa ‘Yarsa Ciki

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Ogun sun cafke wani mutum mai suna Julius Ochim dan shekara 45 da haihuwa, sakamakon yi wa diyarsa ciki kuma har tama haifi diya mace. An kama magidancin ne yayin da diyarsa ta kai karar sai a ofishin ‘yan sanda na sashin Shagamu. Wata majiya ta bayyana wa ‘yan sanda cewa magidancin ya kai tsawan shekara takwas yana lalata da diyarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da cefke magidancin a ranar Talata, ya kuma bayyana wa majiyarmu cewa “mahaifin ya fara lalata ne da diyarsa tun bayan mutuwar matarsa wato uwar yarinyar a shekara ta 2009.” Oyeyemi ya kara da cewa, yarinyar ta sanar wa ‘yan sanda cewa ta samu ciki tare da mahaifinta kuma ma har ta haifi diya mace tun shekara uku da suka wuce. Ya ce “ ta ci gaba da cewa mahaifinta ya yi amfani da abubuwan al’ada yana kwanciya da ita.”

Oyeyemi ya ce lokacin da ‘yan sanda suka samu labarin aukuwar lamarin, sai jami’an sashin ‘yan sandar  Shagamu da kuma Aduroja Moses suka goranci bincike a gidan da abun ya faru inda a nanne aka samu nasarar cafke magidancin. Ya kara da cewa, binciken ya nuna cewa tabbas ya aikata laifin kuma shi ma ya amsa lalle ya aikata amma ya ce aikin shaidan ne.

Ya ci gaba da cewa “ ya bayyana cewa lalle yana kwanciya da ita tun bayan rasuwar matarsa, ya kara da cewa, ya samu matsala da yarinyar tun lokacin da ta fara bin maza kuma tana masa ikirarin cewa tana son ta yi aure.

Oyeyemi ya ce mahaifin ya yi kokarin yana yarinyan nasa yin aure domin ya ci gaba da lalata da ita. Ya kuma kara da cewa kwamishinar Jihar Ahmed Iliyasu ya bada umurnin da a baida magidancin sashin binciken manyan laifika dake Abeokuta.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: