DPP Za Ta Kawo Canjin Da Manyan Jam’iyyu Ba Su Iya Kawo Wa Ba - Juliet Ogbo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

DPP Za Ta Kawo Canjin Da Manyan Jam’iyyu Ba Su Iya Kawo Wa Ba – Juliet Ogbo

Published

on


Wata ‘yar takarar kansila daga mazabar Zuba da ke karanar hukumar Gwagwalada a yankin Abuja, karkashin inuwar jam’iyyar DPP, Juliet Ogbo ta bayyana cewa, jam’iyyar da take ciki wadda ake kallonta a matsayin karamar jam’iyya za ta kawo  canjin da manyan jam’iyyu irin su APC da PDP ba su iya kawo wa al’ummar kasar nan ba.

Juliet ta ce, kyakkyawar manufar jama’iyyar ya sa ta shiga cikinta, da kuma kyakkyawan fatan taimaka wa al’ummar wannan mazaba ta zuba, wadda ta ce, zaben da suka yi a baya ya zama zaben tumun-dare. Domin kuwa akwai abubuwa da dama da al’ummar ke bukata amma jam’iyya mai mulki ta yi watsi da wadannan bukatu na su. Ta bayar da misali da yadda hanyoyin cikin gari suka lalace, wadanda ya kamata karamar hukuma ta yi musu ciko yadda al’umma za su ji dadin zirga-zirga, amma hakan ya gagara, haka nan al‘ummar ke fuskantar matsaloli wajen kai komonsu a wannan yanki .

Saboda haka kamar yadda ta ce, daga cikin manufarta shi ne ta samar da hanyoyin da al’ummar yankin za su ci ribar dimokaradiyya, su kuma amfana da arzikin da Allah ya yi wa yankin.

Juliet ta tabo batun matasa ta mata wadda ta ce, su ne jigon al’umma, amma wannan gwamnati musamman a wannan yanki na su ta ce an yi watsi das u, an ki taimaka musu yadda za su samu ci gaba a rayuwarsu. Saboda haka ita ce, matukar ta samu nasara za yai tafiya da mata da matasa ba tare da nuna bambancin addini ko harshe ba. Sannan ta ce za ta yi kokarain samar da hanyar da al’ummar yanki za su amfana da ilimi musamman ma ‘yayan talakawa.

Saboda haka al’ummar kasar nan na bukatar canji, canji kuma ba da baki ba, canji a aikace, saboda haka jam’iyyar APC ta yi ta ikirarin canji, amma ba a gani a kasa ba. Don haka ta ce, su irin canjin da za su kawo ba na, surutu a baki ba ne, canji ne da al’umma za su tabbatar da amfana  daga mulkin dimokaradiyya.

Haka kuma wani babban kuskure da Juliet ta nuna na wadanda ke kan karagar muliki a halin yanzu shi ne, yadda su kauracewa mutanen mazabarsu, ba sa zuwa cikinsu domin sanin halin da suke ciki, ballantana su magance musu matsalolin da suka dame su.

Saboda haka ta ce, matukar al’umma sun zabe ta a matsayin kansila daga wannan mazaba ta zuba, ba za ta taba zama butulu ba, kullum za ta kasance tare da jama’arta domin jin sanin halin da suke ciki da nemo bakin zaren warware dukkan matsalolin da suka addabe su.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!