Gwamna Bai Mana Adalci Ba A Zaben Fid Da Gwani Na Sanatan Bauchi Ta Kudu -Ahmed Shu’aibu — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Gwamna Bai Mana Adalci Ba A Zaben Fid Da Gwani Na Sanatan Bauchi Ta Kudu -Ahmed Shu’aibu

Published

on


Daya daga cikin wadanda suka fito neman jam’iyyar APC ta tsaida su domin neman cike gibin Sanatan Bauchi ta Kudu, wato Alhaji Ahmed Shu’aibu wanda aka fi sani da ‘Raba Gardama’ ya yi zargin cewar gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abubakar bai yi adalci wajen fid da dan takarar jam’iyyar ba, yana mai bayyana cewar an kimtse wadanda ake son a tsaida tun kafin lokacin zaben.

Dan takarar dai ya ki amincewa da shan kayen da  ya yi shi da wasu shida da suka fito neman kujerar, ya bayyana cewar an tafka rashin adalci tuburan a lokacin zaben, inda ya ce sun aike da takardar koke zuwa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa don a soke zaben da aka yi na fid da gwani.

Ahmed Shu’aibu ya bayyana haka ne a jiya Juma’a a a wani taron manema labaru da ya yi a sakatariyar ‘yan jaridu da ke Bauchi, ya bayyana cewar gwamna da mutanen gwamna ne suka yi abun da ransu yake so, a bisa haka ne ya nuna gayar damuwarsa kan yadda gwamnan ya shiga cikin sha’anin jam’iyyar hadi da aiwatar da son rai.

Ta bakinsa, “Mun taba ganawa da gwamna kan yadda za a yi mu amince don a cire dan takara daya a cikin mu ‘yan takara takwas; domin wai kada a hargiza jam’iyya. Sai muka ce in ka ji zancen hargiza jam’iyya to ba a yi adalci bane, idan aka yi gaskiya aka yi adalci kowa zai karbi abun da aka yi. Daga nan ya yi ta mana alkawarin cewar shi dai baya da wani dan takara daga cikinmu, duk wanda ya ci za su mara masa baya. Daga nan muka amince,” In ji dan takarar

Ya kuma shaida cewar sai kuma suka samu akasin hakan daga shi gwamnan, don haka ne suka sanar da cewar babu adalcin da ya wakana a lokacin fid da gwanin, “Wakilan da suka gudanar da zabe ‘Delegate’ yadda aka tsara tun daga wajen ka san an shirya rashin adalci; a duk fadin dakin zaben nan aka ce kowani dan takara an ba shi ‘agent’ guda daya da zai sanya masa ido kan zaben, ta yaya mutum daya zai sanya ido a akwatina bakwai a lokaci guda? Ka ga tun daga nan an shirya rashin adalci,” A cewar Ahmed

Dan takarar da ya so zama Sanatan  ya kuma bayyana cewar a bisa wadannan dalilan ne ya rubuta wa shugaban jam’iyyar korafi inda yake neman ya soke zaben domin ba a yi adalci a ciki ba, yana mai bayyana cewar ba za su amince da zaben da aka ce an gudanar ba, “wannan zaben da aka ce an yi, sam ba a yi ba; zabe ne wanda gwamna ya ce a yi kaza a yi kaza. Ya bayar da umurni ya kuma sanya ma’aikatansa a wurin zaben duk suna daga cikin kokenmu da muka aike wa shugaban jam’iyyar har da sunayen mutanen gwamna da suka yi wa wajen zaben kawanya ana ganinsu suna zaune suna rubuta kuri’a, idan delegate ya zo baida izinin rubutawa sakamakon zaben da suke so akasin wanda wakilai suke son zaba. Don haka ne na fito na sanar da duniya abin da aka yi. Wannan dalilin ne ma ya sanya tun kafin a gama zaben na fita abu na,” In ji Shu’aibu

Ya bayyana cewar kuma ba zai amshi kaddara ba, don haka ne ya tashi tsaye bidar hakkinsa, “Wannan daukan kaddarar ba mu zo wajen dauka ba. yanzu muna neman a ba mu hakkinmu ne kuma ba mu gamsu da wanda aka zaba ba, domin ba a yi zaben ba.

“Wannan zaben muna son a kashe ta; duk da karantowar lokaci muna son a yi mana wannan,” A cewar shi

Dan takarar ya kuma bayyana cewar, “Ni fa akwai ‘yan uwana da dangina a cikin delegate din nan, an ki yarda su zabi abun da suke so, abin da ake rubutawa kawai shi ne Lawan Yahaya Gumau ko Danjuma Dabo,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan jarida.

Ya yi tsokacin cewar sune suka yi yaki aka kafa APC don haka ba za su fita daga cikin jam’iyyar ba, amma za su ci gaba da neman adalci, ya kuma bayyana cewar zuwar da shugaban kasa ya yi don daka hanun wanda aka fidda tsararren abu ne aka kai wa shugaban kasa, “Mutan ba zai boye rashin gaskiyar da ya tafka ba, sannan su gudu su je su dauko shugaban kasa. In kuna jin shi shugaban kasar da ya samar wa kansa da nagarta da soyayyar da ake masa ai ba a yau ya samu ba, ya jima da samu a sakamakon gaskiyarsa; muna son Buhari kuma za mu iya binsa ko ina,” A cewarsa

Ahmed Shu’aibu ya bayyana cewar yanzu haka zai yi cancanta a kowani bigire domin wanzuwar adalci da kuma ci gaban kasa. Ya kuma nemin shugaban jam’iyyar na kasa ya binciko hadi da yin adalci.

Wakilin LEADERSHIP A YAU, ASABAR ya labarto cewar shi wannan dan takarar ya yi korafin nan ne dai kwana guda bayan da shugaban kasa Muhammadu  Buhari ya zo Bauchi gami da daga hanun wanda aka fidda wato Lawan Yahaya Gumau. Sannan kuma, INEC ta ware ranar 11 ga watan Agustan nan domin gudanar da zaben cike gurbin Sanatan Bauchi ta Kudu.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!