Majalisar Kebbi Ta Ki Amince Wa Da Sunan Wadda Za A Ba Babbar Mai Shari’a — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Majalisar Kebbi Ta Ki Amince Wa Da Sunan Wadda Za A Ba Babbar Mai Shari’a

Published

on


‘Yan majalisar dokoki ta jihar Kebbi sun ki amince wa da a nada mai  rikon mukamin  babbar mai shari’a ta jihar Kebbi , mai shari’a Asabe kuratu, a matsayin mukamin babbar mai shari’a ta jihar, wannan kuwa ya biyo bayan ta yi wani abu cikin satifiket nata na kammala makarantar firamare.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar sun nuna kada a amince da wadda aka mika wa majalisa sunanta, shugaban masu rinjaye ne na majalisar Alhaji Bello Yakubu wanda yake wakiltar mazabar Birnin Kebbi ta kudu, wanda kuma ya samu goyon bayan Alhaji Hamza Bello wanda yake wakiltar mazabar Danko Wasagu ta yamma, a wani zaman  da ‘yanmajalisar suka yi, shugaban majalisar Jihar Alhaji Muhammadu Kamba.

A wata ‘yar gajeruwar magana da ya yi  wa ‘yan majalisar, ya ce, majalisar ba za ta taba amince wa da sunan duk wanda aka bada ba, a  kuma ce takardar shaidar kammala makarantarsa akwai alamar tambaya.

‘’Wannan majalisar ba za ta amince da sunan da aka turo mata ba, muddin aka gane kuma  cewar takardun kammala makarantun shi da akwai matsala. Yanzu kuma ya rage wa gwamnati ta yi tunanin sunan da za ta sake turowa majalisa’’.

Ana iya tunawa dai ita mai rikon mukamin babbar maishari’ar gwaman  jihar Kebbi ya nada ta cikin watan Oktoba na 2017, wannan kuma ya biyo bayan ritayar mai shari’a Ibrahim Mairiga.

 

 

 

 

 

 

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai