An Yi Gangami A Kaduna Kan Ayyukan SUBEB — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

An Yi Gangami A Kaduna Kan Ayyukan SUBEB

Published

on


An gudanar da taron karawa juna sani ga kungiyoyin al’umma a kan yadda UBEC/SUBEB ke gudanar da aikinta da makarantu Sabon Gari/Giwa/Kagarko da ke jihar Kaduna, wanda cibiyar cigaba da kuma binciken dimukradiyya, CEDDERT, ta shirya karkashin Gidauniyar Mac Arthur.

Wakilinmu na daga cikin manema labarai da suka halarci wajen ga kuma abin da ya aiko mana a wannan wake kamar haka.

Bayan halartar manyan baki da suka hada da jami’ai daga SUBEB da UBEC da kuma masana daga cibiyar CEDDERT da shugabannin kungiyar iyayen yara da sarakuna da malaman makaranta daga kananan hukumomi da suke a cikin tsarin da manazartan suka fitar a fadin jihar Kaduna.

Bayan tabbatar da dukkan baki sun halarci dakin taron da a ke kira ‘Center for Edcellence’ da ke harabar jami’ar Ahmadu Bello, sai aka gabatar da kasidar makasudin taron mai take kamar haka: ‘makasudi da kuma manufar kula da yadda a ke amfani da kudaden UBEC da SUBEB ke yi a jihar Kaduna’

Bayanin kasidar ya fara ne da gabatarwa, “Aikin bibiya da kuma tabbatar da cewa ana yin amfani da kudaden UBEB da SUBEB ke yi a jihar Kaduna a na gudanar da shi ne domin tabbatar da yaki da cin hanci da yake gudana a kasa baki daya, wanda wannan na da mutukar muhimmanci a wajen samar da ayyuka ga jama’a. Yanayin yadda dalubai ke jarabawa ko yanayin cin nasararsu a jarabawa musamman manyan jarabawowi na kasa na nuni da cewa yanayin ilimi mai kyau ya fadi domin hakan ya fito fili a irin yanayin tabukawar dalubai a jarabawowin WAEC, NECO da JAMB. Mafi yawancin daluban mu suna kasa cin darussan Lissafi da Turanci. Wannan kuwa yana faruwa ne a dalilin abubuwa masu yawa kamar rashin cikakkun kayan da ake bukata a wajen koyar da karatu da kuma rashin ingancin koyarwa. Kamar yadda a ka bayyana a cikin littafin ‘Nigerian Economic Crisis: Causes and Solution’ (1985) bangaren ilimi yanzu ya zama wani waje na lunlunka dukiya ta hanyoyin da basu dace ba. Ana ba da ayyukan da ake biyan kudinsu amma ba a aiwatar ba. Ana biyan albashi ga ma’aikatan da ba su. Akwai ma makarantun da ke cikin kundin gwamnati amma a hakika ba su. Cin hanci ya cika ko’ina ba wai kawai a bangaren ilimi ba. Ayyukan UBEC ma a cikin irin wannan yanayi ya ke kuma abu ne mai wuya ta iya tsallakewa. To amma gwamnatin jihar Kaduna ta nuna kokarinta wajen ganin an samar da inganci da kyakkyawan yanayi da bin doka a cikin sha’anin mulki, don haka ta samar da damar shigowa wannan fage. Kari a kan haka kuma shine suma jama’ar kasa sun shirya su tabbatar da cewa sashen ilimi yana tafiya yadda ya kamata ya yi.

“Makasudin wannan kasida dai shi ne na daya ta nuna yadda ake yin amfani da kyau da kudaden da ake warewa bangaren ilimi daga firamare zuwa aji uku na karamar sakandire, na biyu kuma ta nuna kokarin gwamnatin jihar Kaduna wajen inganta ilimi a kashin kanta tare kuma da hada kai da wasu cibiyoyin na tarayya.

“Na uku kuma ta nuna irin kokarin gwamnatin tarayya da ta jiha wajen inganta ilimin firamare da sakandire, a cire cin hanci a yayin zartar da ayyuka, ta kuma karfafa al’umma su kula da UBEC/SUBEB, ayyukanta da goyon gwamnatin jiha a ayyukanta domin infanta ilimin firamare zuwa aji uku na karamar sakandire.

“Ayyukan Mac Arthur, musamman bayan yin la’akari da yadda ilimi ya fadi a yanzu, gidauniyar Mac Arthur ta samar da wani shiri domin kawo karshen abin da kuma gano hanyoyin fa za a cire cin hanci daga cikin tsarin ta yadda kudin da aka ware ma ilimi za a yi abinda ya dace da su. CEDDERT da wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba an sa su duba yadda wadannan manufofi za a iya cimma su. Ana dai tsammanin CEDDERT da wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba (NGO’s) za su bullo da hanyoyin shigowa da al’umma domin tabbatar da zartar da ayyukan SUBEB/UBEC domin tabbatar da cewa shirye-shiryensu an zartar da su yadda aka tsara. Domin yin hakan, CEDDERT tana amfani ne fa tsari kamar haka:

“CEDDERT tana tabbatar da cewa ta samar da horo ga wadanda suke da hannu a cikin aikin domin su iya samun haduwa da al’ummu manya, ta hanyar tattarowa da samar da bayanai a manyan tarurruka a garuruwa. Abinda ake bukata dai shine a tattaro al’ummu su goyi bayan wadanda ke da hannu a cikin lamarin. Kuma abinda ake so shine a samu hadin kai tsakanin masu hannu a al’amarin da kuma mutanen al’ummu ta hanyar samar da kudade da aiwatar da shirye-shirye.

“CEDDERT dai na da ra’ayin domin a iya cimma wadannan manufofi, dole a samar da hanyoyin samun bayanai idan an yi wasu abubuwa ba daidai ba. Wannan kuma na da bukatar samun goyon baya daga ma’aikatar iyaye ta hanyar doka. Haka kuma ana da bukatar ma’aikatar ilimi ta kasa ta samar da wata takarda da za ta mayar da shigowar al’umma cikin ayyukan UBEC/SUBEB dole.

“Kasancewarta wata ginshiki a cikin al’ummunku, CEDDERT na neman shigowarku cikin wannan al’amari, shigowarku cikin wannan aiki zai tabbatar da cewa abubuwan da aka tsara cimmawa na wannan aiki an cimmasa cikin nasara.”

Bayan wannan kasida da aka gabatar an ci gaba da gabatar da wasu kasidun masu take daban daban.

Akwai kasidun da aka gabatar masu take kamar haka, “Yadda wannan aiki ke gudana” “Tsarin da ake amfani da shi wajen bin diddiki” “Yadda za a taimaka wajen shigowar al’ummu da kuma dorewar ayyukan SUBEB” “Rawa da kuma hakkin da ya rataya a wuyan masu kula da kwamitocin makarantu” “Rawar da masu kula da al’ummu za su taka wajen zartar da ayyukan SUBEB” “Samar da hadaka tsakanin CBO’s, FBO’s da kuma sarakunan gargajiya a wajen kula da ayyukan SUBEB” “Shigowar masu hannu a cikin lamarin daga al’ummu da kuma kula da ayyukan SUBEB: Hanyar tabbatar da samar da nagarta a cikin ayyuka”

Bayan gabatar da wadannan kasidu, wakilinmu ya sami zantawa da FarfesaFarfesa Mustafah Gwadabe, wanda shine jagoran masana daga CEDDERT inda ya ce “Wannnan taro babu sa hannun gwamnati a cikinsa amma gidauniyar MacArthur ce ta dauki nauyisa mu kuma NGO ne wato Centre for democracic development reseeach and treanig muke bada horo ga al’ummar don a wayar masu da akai akan su san hakinsu da gwamnati ke bayarwa don amfanar su bisa dalilan da da hujjoji da ake samu mai nuna cewa wasu hakkokin da gwamnati ke turowa dan amfanar al’uma yana karkata zuwa wani waje.

“Hakan ya sa mu ke wayarwa da jama’a kai don hakan munaga zai rage yawan cin hanci da rashawa a tsakani al’ummar kasa baki daya kuma wannan shiri ana gabatar dashine a kananan hukumomin jihar kaduna ne amma mu CEDDERT mun takaitu ne a karamar hukumar Sabon Gari da Giwa da Kagarko a yanzu haka.

“Fatanmu shine jama’a su gane hakinsu kuma su fahimci inda hakin nasu ke fitowa kuma susan in an zaluncesu ina za su kai kukansu don a magance masu abin da ke damunsu.

“Kuma mun gode Allah ga shi dukkan wanda mu ka gaiyyata sun zo, komai na tafiya.”

Advertisement
Click to comment

labarai