Gwamma Na Bar Siyasa A Kan Na Bar Jam’iyyata –Makarfi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Gwamma Na Bar Siyasa A Kan Na Bar Jam’iyyata –Makarfi

Published

on


Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma mai neman takarar shugabancin Najeriya, Sanata Ahmed Makarfi, ya bayyana cewa, gwamma ya bar harkokin siyasa bakidaya a kan ya fice daga cikin jam’iyyarsa ta PDP idan bai samu tikitin tsaya wa takarar ba.

Makarfi ya bayyana hakan ne a Minna babban birnin jihar Neja ranar Asabar bayan da ya kai ziyarar neman shawarwari hedikwatar jam’iyyar da ke Minna da kuma gidan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya.

“Ba na shakku ko tunanin barin PDP zuwa wata jam’iyya. Gara na bar harkokin siyasa bakidaya kan hakan, domin ban yarda da fita daga cikin jam’iyya ba,” in ji shi.

To, sai dai kuma ya bayyana cewa, ba laifi ba ne ficewa daga cikin jam’iyya, illa dai kawai hakan ya saba da ra’ayinsa ne kadai.

A ta bakinsa “na yi wata magana a Lokojo wacce za a ga tamkar kwan-gaba-kwan-baya ne. To, Ina goyon bayan wadanda su ka shigo jam’iyyata dari bisa dari. A takaice ma dai na yi hasashen cewa bayan kammala zabukan shugabannin jam’iyyar APC za a samu irin wannan ficewar da dama. Har yanzu mu na tsammanin wasu ma za su sake biyo bayan wadanda su ka fito din, amma kalubalen shi ne ta yadda za a iya gudanar da wannan nasarar.

“Idan mu ka yi amfani da ita yadda yakamata, to mu za ta amfana, amma idan mu ka gaza yin hakan, za a samu koma-baya. Ni dai na san ba zan iya barin jam’iyyata na koma wata ta bisa kowane dalili.”

Ya kara da cewa, PDP ta na da isasshen gurbin da za ta iya adana duk wadanda su ka shigo cikinta. Don haka ya yi kira ga jagorancin jam’iyyar da ya yi tanadi mai kyau wajen ganin an yiwa wadanda su ka shigo kyakkyawan masauki.

“A shirye mu ke da mu yi sadaukarwa, don amfanin jam’iyyarmu a dunkule da ’yan Najeriya bakidaya,” in ji shi.

Ya yi karin haske da cewa, “shugaban majalisar dattawa, mataimakinsa da kakakin majalisar wakilai an zabe su ne ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Don haka kiran da shugabancin APC ke yi na su sauka daga mukamansu saboda sun bar jam’iyyar a yanzu abu ne da bai dace ba kuma ya saba wa doka da tsarin mulkin kasa.”

Game da burinsa na shugabancin kasar, sai ya yi ikirarin cewa, hatta layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna da gwamnatin APC ke alfaharin ginawa, abu ne wanda shi Makarfin ya samar da shi tun lokacin tsohon shugaban  kasa Olusegun Obasanjo lokacin da ya shugabancin wani kwamiti.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!