Idan A Ka Samu Barkewar Rikici Laifin ’Yan APC Ne, Cewar Sanatocin PDP — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Idan A Ka Samu Barkewar Rikici Laifin ’Yan APC Ne, Cewar Sanatocin PDP

Published

on


Ganin yadda jam’iyyar APC ke faman hankoron ganin an sauke shugabannin majalisar dokoki ta kasa bisa fita daga cikin jam’iyyar mai mulki, sanatocin babbar jam’iyyar adawa ta kasa, PDP, sun bayyana cewa, idan har a ka samu barkewar rikicin da ya kai ga karya da doka da oda, to b alaifin kowa ba ne face na ’yan jam’iyyar APC.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da sanatoci masu wakiltar jihohin Bauchi da Kwara, Sanata Isa Hama Misau da Sanata Rafiu Ibrahim, su ka sanya wa hannu a jiya Asabar, inda su ka ja kunnen sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu, Sanata Abu Ibrahim da sauran sanatocin APC kan tayar da kura a cikin majalisar bisa ficewar shugabannin majalisar dokokin daga APC, wacce ke mulkin kasar.

Misau da Rafiu, wadanda su na daga cikin sanatoci 14 da su ka bar APC zuwa PDP, sun yi kira ga abokan aikin nasu da su amshi kaddara su bar majalisa ta cigaba da aikinta yadda ya kamata a lokacin da za ta koma aikinta ranar 25 ga Satumba, 2019, bayan ta kammala hutu.

Sai kuma su ka yi gargadin cewa, daidai su ke da duk wanda ya nemi ya hana su rawar gaban hantsi. Don haka su ka nemi jami’an tsaro da su yi shirin ko-ta-kwana.

Idan dai za a iya tunawa, Sanata Abu Ibrahim, a wata hira da ya yi da manema labarai cikin har da LEADERSHIP, ya bayyana cewa, ya kamata shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya sauka daga mukaminsa tunda dai ya bar jam’iyyar da a ka zabe shi a cikinta, ba don komai ba sai don a zauna lafiya.

Daga nan sai ya bayyana cewa, akwai yiwuwar majalisar ta koma aikinta kafin wa’adin ranar komawar, don yin abinda ya kamata.

 

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!