Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 5 A Ondo

Published

on

Mutane 5 sun rasa rayukansu yayin da wadansu kuma suka ji mummunar raunika sakamakon hatsarin mota a mahadan da ake kira Agbabu dake babban titin Ore-Okitipupa cikin karamar hukumar Odigbo a Jihar Ondo ranar Juma’a da yamma. Mai magana da yawun ‘yan sandar Jihar Mista Femi Joseph ya ce, hadain ya faru ne da karfe 6.30 na yamma. Ya kuma kara da cewa “ biyar daga cikin mutanan sun mutu nan take uku mata biyu kuma maza. Wani daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu ya labarta muna cewa, direbar motar mai suna Daniel shi ya jawo hadarin, domin ya bar hannunsa inda ya fada ma matar da take zuwa daga Okitipupa sai ya buge ta. “Muna tunanin direban ya sha giya saboda yadda yake tuki kuma yana karkata wa zuwa daya hannun da bana shi ba. Ya gudu lakacin da hadarin ya auku kuma yar yanzu muna neman sa.” Ya kara da cewa, karu ne ya faru tsakanin motan bas mai lamba Legas MT 138KJA da kuma mota kirar Toyota Abensis mai lamba Ondo BDR 599 AA, ya ce dukansu suna kan hannunsu dai-dai. Duk da haka, a labarin da muka samu daga ofishin rundunar jami’ai masu kiyaye haduruka sun nuna cewa mutane uku sun mutu a hadarin. A Na Samun Karuwan Mata Masu Mu’amala Da Kwayoyi A Kano Da Katsina Daga Yusuf Shuaibu Kungiyar mata daga Arewa sun yi nuni da cewa a na samun karuwan mata masu mu’amala da muyagun kwayoyi a Kano da Katsina. Sun kuma shawarce Gwamnatin Tarayya da ta dau mataki a kan wannan mummunar dabi’a. Kungiyar ta bayyana haka ne a garin Abuja wajen wani taro, inda ta ce, matan wadannan Jihohi guda biyu suna mu’amala ne da muyagun kwayoyi sakamakwan “ takaici, koya daga wasu da kuma rashin ilimi.” Shugaban kungiyar Miss Aisha Hussain ta ce, za a shakan wannan matsala ne kawai in dai gwamnti tare da hadin kan kungiyoyi masu zaman kansu wajen fadakar da jama’a. Ta kuma kara da cewa babbar matsalar dake damun mata a Arewacin kasar nan a yanzu ta ci mu’amula da muyagun kwayoyi. Mun gano cewa a halin yanzu mata sun fi maza mu’amala da muyagun kwayoyi a cikin Arewacin kasar nan a jihohin Kano da kuma Katsina.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: