Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Sojojin Sun Cafke Mutum Biyu Bisa Laifin Damfara

Published

on

A ranar Lahadi ne rundunar sojojin Nijeriya suka samu nasarar cafke wadan su mutane guda biyu saboda laifin daukan hankalin mutane a kan daukan ma’aikata a cikin hukumar sojojin Nijeriya. An dai boye sunayan wadanda ake zargin, sannan kuma an gabatar da su a gaban mukaddashin kakakin rundunar sojojin Nijeriya dake Zariya cikin Jihar Kaduna mai suna Lt. Adekunle Adeyemi.

“Wadannan mutane sun tsunduma ne wajen damfarar mutane tare da karbe musu kudade domin su sama musu aiki a cikin rundunar sojojin Nijeriya. “Suna amfani ne da kafafan sadarwa wajen amshewa mutane kudadensu tare da yi masu alkawarin za su taimake su domin su samu gurbin aiki a cikin rundunar sojojin Nijeriya,” a cewar kakakin.

Adeyemi ya ce a cikin wadanda aka kama harda wanda aka tabe kama wa a ranar 29 ga watan Yuli kusa da runduna na Chindit. Ya kara da cewa, Kaman abin mamaki ne saboda wacan kaman bai zama darasi a gare shi ba. “Wadanda ake zargin suna da’awar cewa suna aiki ne tare da Abubakar Sadik Musa da kuma Lawal Bala Abdullahi wadanda suke cikin rundunar sojojin Nijeriya.

“ Na je Jihar su Abubakar Sadik Musa da kuma Lawal Bala Abdullah sai na samu duk an kore su a cikin rundunar ta sojojin Nijeriya. “Wadanda aka cefke an shaida dai sun damfari mutane takwas kudi naira miliyan 1.3 wanda suka raba tsakaninsu,” inji Adeyemi. Kakakin ya ce sun amso kudade wanda ya kai naira 163,000 daga wajen wadanda aka kama.

Ya kuma tabbatar da cewa shiga aikin sojojin Nijeriya dai kyauta ne sai dai kawai fom ne muke sawa a yanar gizo amma muna tantance kowani mai sha’awar shiga aikin soja ne a jihohinsu. Adeyemi ya kara da cewa, yana gargadin mutane masu sha’awar aikin soje da su kula sosai don kar su jiga hannun irin wadannan mutane da suke amfani da yanar gizo suna damfarar mutane. Da suke magana da ‘yan jarida, dayan ya ce yana zaune ne a Rigasa cikin Jihar Kaduna yayin da dayan kuma ya ce, yana zauna ne a layin Isa Kaita duk cikin Jihar Kaduna.

Bayan haka, dukkan su suna zargin junansu da cewa kowanne shi ne ya saka daya cikin wannan harkan damfarar. Majiyarmu ta labarta mana cewa kowannan su ya amsa kudin da ya kai naira 250,000 a hannan mutanan nan takwas masu sha’awar shiga aikin soja.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: