Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Ta Kashe Mijinta Saboda An Kirasa A Waya

Published

on

‘Yan sanda a Jihar Legas sun cefke wata mata mai suna Damilola Ayeni ‘yar shekara 23 da haihuwa sakamakon kashe majinta mai suna Olumide a layin Bamgbose cikin Island dake Jihar Legas.

Majirmu ta labarta mana cewa, sun yi aure shekara biyu da suka wuce kuma suna da yara guda biyu, sun dai samu rashin jituwa ne tun ranar Juma’a a cikin gidansu.

Matan ta soki mijinta dan shekara 36 da wuka a kirjinshi, bayan aukuwar lamarin an garzaya da shi babban asibitin Island dake jihar Legas inda nan ne rai ya yi halinsa.

Baban marigayin mai suna Sunday Ayeni shi ne wanda ya sanar wa ‘yan sanda faruwar lamarin ranar Lahadi. Wani mutum mai suna Ikale dan asalin jihar Ondo, shi ne ya yi kokarin sulhunta su amma sai wani daga cikin ‘yan’uwan marigayin yay aha shi. Baban marigayin ya kara da cewa, matan yaron nasa ta kashe shi ne bisa makirci irin nasu na mata. Sunday ya ci gaba da cewa “yarona yana aiki a babban asibiti dake Island ta jihar Legas bangaran wajen shan sayar da magani yayin da nima nake aiki a asibitin amma bangarin masu gadi, a inda nan ne ya auri wannan matan.

“Lokuta daban-daban suna samun rashin fahimta kuma yarona ya kawo min karanta. Na gaya masa cewa su je su shirya kansu, amma mutane sun nuna cewa a rabasu saboda zaman babu dadi a tsakaninsu.

“ A ranar Juma’a, bayan ya tashi daga aiki sai ya tafi wajen rawa kuma har ya kira matansa ta wayan tarho sun yi magana.

“Bayan ya dawo gida ne sai matansa ta tsare shi a kofa, tana cewa lokacin da ya kirata a wayar tarho ta ji muryan mace. Wannan shi ne dalilin da ya sa ta soke shi da wuka a karjinsa kuma nan take ya mutu. Mun amsa yaran guda biyu daga wajenta ciki har ‘yar wata uku.” Yana bukatar abi masa hakkinsa, domin ya kwatanta dan nasa a matsayin mutumin kirki da kuma saukin kai.

Wakilinmu ya labarta mana cewa, matan ta fada wa ‘yan sanda cewa ta kashi shi ne wajen kare kanta, domin shi ne ya tsokane ta. Wakilinmu ya kara da cewa “ matan ta cewa marigayin ya kirata da misalign karfe daya na dare sai ba ta dauka ba a ranar Asabar, sai ya tambaye ta a ina ne ta ajiye wayanta? Daga nan ne ya fara zargin ta, sai ya tafi kicin ya dauko wuka, garin kokarin kare kanta ne sai ta caka masa a kirginsa.” Majiyarmu ta ce, ‘yan sandar reshen Lio sun cefke ta amma daga bisani an mai da ta sashin binciken manyan laifuka ta Yabe dake cikin Jihar.

Jami’in hudda da jama’a na rundunar ‘yan sanda CSP Chinke Oti ya ce, kwamishinan ‘yan sanda Edgal Imohimi ya yi bakin cikin da faruwar lamarin.

Ya kara da cewa “ narar Lahadi da sassafe ne muka samu labarin cewa wata mata mai suna Damilola Ayeni ta kasha mijinta da wuka mai suna Olumide Ayeni kuma an garzaya da shi babban asibitin Island dake Jihar Legas amma rai ya yi halinsa.

“CP ya shawarci ma’aurata da su dunga sasanta kawunansu cikin ruwan sanyi ba sai ya kai ga kisa ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: