Ya Kamata APC Ta Fuskanci Matsalolin Ta Na Cikin Gida- inji Aisha — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Ya Kamata APC Ta Fuskanci Matsalolin Ta Na Cikin Gida- inji Aisha

Published

on


Hajiya Aishatu Ibrahim Dan Gaskiya ita ce Shugabar mata ta jam’iyyar PDP yankin Neja Ta Arewa, a zantawarta da wakilinmu Muhammad Awwal Umar ta yi tsokaci kan canja shekar Sanata Bukola Saraki, Kwankwaso da gwamnan Sokoto Tambuwa. Ga gajeruwar hirar.

Jam’iyyar APC ta bukaci shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola da ya sauka daga kan kujerar sa ganin ya bar jam’iyya mai mulki. Wani karin haske za ki yi akai.

Maganar Sanata Bukola ya bar kujerar sa na shugabancin majalisar bai ma taso ba, domin lokacin da wannan guguwar Buharin ta taso gwamnonin PDP biyar zuwa shida ne suka canja sheka zuwa APC kuma ba wani gwamna da PDP din tace ya bar kujerar sa tunda muna mulkin dimukuradiyya ne. Bukola zaben shi aka yi a matsayin shugaba kuma mafi rinjayen da suka zabe shin nan ‘yan PDP ne, to daman APC tayi shiru saboda ta san za ta anfana da hakan. Yau sanata Bukola shi ne na uku a kasar kamar yadda tsarin mulki ya nuna kuma zaben sa aka yi kamar sauran dan haka mai makon APC ta tsaya kame-kame ya kamata ta huskanci matsalolin ta na cikin gida da ke damunta, ba wani doka zuwa yanzu da yace dan an yi ma ba daidai ba ka canja sheka a kore ka daga mukamin ka tunda ba nada ka aka yi karfin kuri’a ne ya kai ka kamar sauran.

Idan APC da gwamnatinta ba su manta ba fa cewar sanata Bukola asalinsa dan PDP ne, idan abinda yasa ya bar PDP din zuwa APC yasa kuma yau bai gamsu da irin wannan dalilin APC din ba, yana ganin hanyar da PDP din ke bi itace gyara ka ga ke nan yana wannan ne dan cigaban dimukuradiyya da al’ummar sa.

Ba iya ganin irin wannan rashin alkiblar ‘yan siyasa ka iya mayar da hannun agogo baya musamman ganin yadda canja sheka ke son zama wani shika-shikan siyasar kasar nan.

Bari mu je kan maganar canja sheka da ka ke magana akai, lokacin zabukan 2015 APC tayi yakin zabe ne da kawo karshen ta’addanci da inganta tattalin arzikin kasa wanda a wancan lokaci shi ne babban abinda talakan da ke karkara ke bukata ganin an hana shi aikin noma, ya kasa samun kwanciyar hankali har yasa ake ganin kasawar gwamnati ce a lokacin ya janyo hakan ko.

To ka duba yau abin da ke faruwa musamman a jihohin Kaduna da Zamfara da Sokoto, har manazarta na cewar adadin mutanen da suka rasa rayukansu kan rikicin makiyaya da manoma ya ninka wadanda suka mutu a lokacin PDP sau shida, in haka ne ina tsaron yake. Ka duba lokacin da ake kashe dubban mutanen karkara gwamnatin tarayya na ta antayawa gwamnatocin jahohi kudi dan magance matsalar tsaron amma misali duk lokacin da wadannan abubuwan ke faruwa wasu gwamnonin APC din na tare da shugaban kasa a Abuja ba wani matakin da gwamnati ke dauka akan gwamnonin, to wannan sai ya tabbatar maka da cewar koda ba kasawar gwamnatin PDP ba ne illa kawai ‘yan adawa sun yi anfani da wannan damar ne kuma hakan yasa masu canja shekar ganin gara su dawo dan gyara kurakuran da aka yi a baya.

Saboda haka daman masu canja shekar kurakurai suka hango a wancan lokacin kuma sun gamsu da matakan da ake dauka yanzu na kawo gyara, shi yasa mu tunanin dawowar dan ayi gyaran da su. Misalin kuri’un da sanata Kwankwaso ya samu lokacin da ya dawo kujerar gwamna karo na biyu, da kuri’un da ya samo wa APC a wannan zagon ya is a ya nuna ma gamsu wa da amintar sa ga jama’arsa, ka ga mu a PDP dole ma mu yi farin ciki  da dawowarsu. Ina da tabbacin dawowar sanata Saraki, Kwankwaso da gwamna Tambuwal alheri ne ga kasar nan, alheri ne ga PDP.

Amma kin yi maganar halin rashin kulawar gwamnoni ga jahohin su, ba ki ganin gwamnan sokoto, Aminu Waziri Tambuwal bai da wani dalilin barin APC ganin ma ita ce ta kawo shi a wannan matsayin.

Indai kana kasar nan kowa yaji dalilansa ai, yace gwamnatin tarayya ta watsar da sakkwatawa kuma ko bayan hare-haren da aka kai a wasu yankunan jihar da ya janyo rasa rayukan al’umma ba wani abu na nuna damuwa ko nunawa jama’ar sokoto daga gwamnatin tarayya, kuma ai ka ji abinda gwamnan ya fadi a irin salon mulkin APC a kasar nan. Shi ke nan an zauna cikin kunci kuma ai ta tafiya hakan.

Shin al’ummar Sokoto ba su bai wa APC din kuri’a ba ne halan, kai koma dai ba su yi hakan ba, su ba ‘yan Nijeriya ba ne halan, ka ga ke nan kishin al’umma da damuwa a kan halin da suke ciki yasa gwamna Tambuwal yin abin kuma abinda ya yi daidai ne. Bai kamata a kasar nan a rika nuna bambancin ba, na san yau da kasar Yarbawa wannan abu ya faru da tuni Buhari ya jefa kafarsa saboda sun fi ‘yan Arewa gata a gwamnatin nan.

Ganin irin wannan turka turkan da ke tasowa, kuma ‘yan PDP ba kwaba ganin za ku iya jawo rudani ga damar da Arewa ta samu yanzu.

Bari in fada ma gaskiya, a Arewa muna da mutane masu nagarta wadanda ko ba PDP suke yi ba muna iya zaben su idan siyasa yazo saboda kusancin su da al’umma da soyayyarsu da Arewa. Bari in baka misalin da tsohon gwamnan Kano, kuma sanatan Kano ta tsakiya, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ban cin ayyukan da ya yi a jihar Kano ko wa shaida ne, ‘yayan talakawa kuma ‘yan asalin jihar Kano da ya baiwa tallafi suka tafi waje su kai karatu nan gaba su ne gatan Arewa, a lokacin da ya ga wani ginshikin addini da yake martaba rayuwar dan Adam, wato aure, ta dauki nauyin auratar da marasa karfi tare da ba su tallafi wannan abin a yaba ne.

Mu a kullun muna tare da mutane masu akidar gaskiya, masu son cigaban kasa da al’ummarta dan da haka ne kawai za a iya samar da tsaro a cikin al’umma.

Yanzu abin da kasar nan ke bukata gwamnatin da za tai wa kowa adalci, a rika taba tattalin arzikin kasa yadda ya kamata ta haka ne kawai za a iya kaucewa rashawa da dagawar martabar tattalin arzikin kasa.

 

Advertisement
Click to comment

labarai